الفتح   سورة  : Al-Fath


سورة Sura   الفتح   Al-Fath
قُل لِّلْمُخَلَّفِينَ مِنَ الْأَعْرَابِ سَتُدْعَوْنَ إِلَىٰ قَوْمٍ أُولِي بَأْسٍ شَدِيدٍ تُقَاتِلُونَهُمْ أَوْ يُسْلِمُونَ ۖ فَإِن تُطِيعُوا يُؤْتِكُمُ اللَّهُ أَجْرًا حَسَنًا ۖ وَإِن تَتَوَلَّوْا كَمَا تَوَلَّيْتُم مِّن قَبْلُ يُعَذِّبْكُمْ عَذَابًا أَلِيمًا (16) لَّيْسَ عَلَى الْأَعْمَىٰ حَرَجٌ وَلَا عَلَى الْأَعْرَجِ حَرَجٌ وَلَا عَلَى الْمَرِيضِ حَرَجٌ ۗ وَمَن يُطِعِ اللَّهَ وَرَسُولَهُ يُدْخِلْهُ جَنَّاتٍ تَجْرِي مِن تَحْتِهَا الْأَنْهَارُ ۖ وَمَن يَتَوَلَّ يُعَذِّبْهُ عَذَابًا أَلِيمًا (17) ۞ لَّقَدْ رَضِيَ اللَّهُ عَنِ الْمُؤْمِنِينَ إِذْ يُبَايِعُونَكَ تَحْتَ الشَّجَرَةِ فَعَلِمَ مَا فِي قُلُوبِهِمْ فَأَنزَلَ السَّكِينَةَ عَلَيْهِمْ وَأَثَابَهُمْ فَتْحًا قَرِيبًا (18) وَمَغَانِمَ كَثِيرَةً يَأْخُذُونَهَا ۗ وَكَانَ اللَّهُ عَزِيزًا حَكِيمًا (19) وَعَدَكُمُ اللَّهُ مَغَانِمَ كَثِيرَةً تَأْخُذُونَهَا فَعَجَّلَ لَكُمْ هَٰذِهِ وَكَفَّ أَيْدِيَ النَّاسِ عَنكُمْ وَلِتَكُونَ آيَةً لِّلْمُؤْمِنِينَ وَيَهْدِيَكُمْ صِرَاطًا مُّسْتَقِيمًا (20) وَأُخْرَىٰ لَمْ تَقْدِرُوا عَلَيْهَا قَدْ أَحَاطَ اللَّهُ بِهَا ۚ وَكَانَ اللَّهُ عَلَىٰ كُلِّ شَيْءٍ قَدِيرًا (21) وَلَوْ قَاتَلَكُمُ الَّذِينَ كَفَرُوا لَوَلَّوُا الْأَدْبَارَ ثُمَّ لَا يَجِدُونَ وَلِيًّا وَلَا نَصِيرًا (22) سُنَّةَ اللَّهِ الَّتِي قَدْ خَلَتْ مِن قَبْلُ ۖ وَلَن تَجِدَ لِسُنَّةِ اللَّهِ تَبْدِيلًا (23)
الصفحة Page 513
(16) Ka ce wa waɗanda aka bari daga ƙauyãwa: "Za a kira ku zuwa ga waɗansu mutãne mãsu tsananin yãƙi (dõmin) ku yãƙe su kõ kuwa su musulunta. To, idan kun yi ɗã'a, Allah zai kãwo muku wata ijãra mai kyau, kuma idan kuka jũya bãya kamar yadda kuka jũya a gabãnin wancan, zai azãbtã ku, azãba mai raɗadi."
(17) Bãbu laifi a kan makãho, kuma bãbu laifi a kan gurgu, kuma bãbu laifi a kan majiyyaci. Kuma wanda ya yi ɗã'a ga Allah da ManzonSa, (Allah) zai shigar da shi a gidãjen Aljanna, kõguna na gudãna daga ƙarƙashinsu. Kuma wanda ya jũya bãya, (Allah) zai azabtãshi, azãba mai raɗãɗi.
(18) Lalle ne haƙĩƙa, Allah Ya yarda da muminai a lõkacin da suke yi maka mubãya, a a ƙarƙashin itãciyar nan dõmin Yã san abin da ke cikin zukãtansu sai Yã saukar da natsuwa a kansu, kuma Ya sãka musu da wani cin nasara makusanci.
(19) Da waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa da zã su karɓo su. Kuma Allah Yã kasance Mabuwayi, Mai hikima.
(20) Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo su, kuma Ya gaggauta muku wannan. Kuma Ya kange hannãyen mutãne daga gare ku, kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya madaidaiciya.
(21) Da waɗansu (ganĩmõmin) da bã ku da ĩko a kansu lalle Allah Ya kẽwaye su da saninSa, kuma Allah Ya kasance Mai ikon yi ne a kan dukan kõme.
(22) Kuma dã waɗanda suka kãfirta sun yãke ku, dã sun jũyar da ɗuwaiwai (dõmin gudu) sa'an nan bã zã su sãmi majiɓinci ba, kuma bã zã su sãmi mataimaki ba.
(23) Hanyar Allah wadda ta shũɗe daga gabãnin wannan, kuma bã zã ka sãmi musanya ba ga hanyar Allah (ta taimakon mũminai akan mai zãluntarsu).
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022