المائدة   سورة  : Al-Maaida


سورة Sura   المائدة   Al-Maaida
وَإِذَا نَادَيْتُمْ إِلَى الصَّلَاةِ اتَّخَذُوهَا هُزُوًا وَلَعِبًا ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ قَوْمٌ لَّا يَعْقِلُونَ (58) قُلْ يَا أَهْلَ الْكِتَابِ هَلْ تَنقِمُونَ مِنَّا إِلَّا أَنْ آمَنَّا بِاللَّهِ وَمَا أُنزِلَ إِلَيْنَا وَمَا أُنزِلَ مِن قَبْلُ وَأَنَّ أَكْثَرَكُمْ فَاسِقُونَ (59) قُلْ هَلْ أُنَبِّئُكُم بِشَرٍّ مِّن ذَٰلِكَ مَثُوبَةً عِندَ اللَّهِ ۚ مَن لَّعَنَهُ اللَّهُ وَغَضِبَ عَلَيْهِ وَجَعَلَ مِنْهُمُ الْقِرَدَةَ وَالْخَنَازِيرَ وَعَبَدَ الطَّاغُوتَ ۚ أُولَٰئِكَ شَرٌّ مَّكَانًا وَأَضَلُّ عَن سَوَاءِ السَّبِيلِ (60) وَإِذَا جَاءُوكُمْ قَالُوا آمَنَّا وَقَد دَّخَلُوا بِالْكُفْرِ وَهُمْ قَدْ خَرَجُوا بِهِ ۚ وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا كَانُوا يَكْتُمُونَ (61) وَتَرَىٰ كَثِيرًا مِّنْهُمْ يُسَارِعُونَ فِي الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَأَكْلِهِمُ السُّحْتَ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (62) لَوْلَا يَنْهَاهُمُ الرَّبَّانِيُّونَ وَالْأَحْبَارُ عَن قَوْلِهِمُ الْإِثْمَ وَأَكْلِهِمُ السُّحْتَ ۚ لَبِئْسَ مَا كَانُوا يَصْنَعُونَ (63) وَقَالَتِ الْيَهُودُ يَدُ اللَّهِ مَغْلُولَةٌ ۚ غُلَّتْ أَيْدِيهِمْ وَلُعِنُوا بِمَا قَالُوا ۘ بَلْ يَدَاهُ مَبْسُوطَتَانِ يُنفِقُ كَيْفَ يَشَاءُ ۚ وَلَيَزِيدَنَّ كَثِيرًا مِّنْهُم مَّا أُنزِلَ إِلَيْكَ مِن رَّبِّكَ طُغْيَانًا وَكُفْرًا ۚ وَأَلْقَيْنَا بَيْنَهُمُ الْعَدَاوَةَ وَالْبَغْضَاءَ إِلَىٰ يَوْمِ الْقِيَامَةِ ۚ كُلَّمَا أَوْقَدُوا نَارًا لِّلْحَرْبِ أَطْفَأَهَا اللَّهُ ۚ وَيَسْعَوْنَ فِي الْأَرْضِ فَسَادًا ۚ وَاللَّهُ لَا يُحِبُّ الْمُفْسِدِينَ (64)
الصفحة Page 118
(58) Kuma idan kuka yi kira zuwa ga salla, sai su riƙe ta bisa izgili da wãsa. Wannan dõmin lalle ne su, mutãne ne (waɗanda) bã su hankalta.
(59) Ka ce: "Ya Mutãnen Littãfi! Shin, kunã ganin wani laifi daga gare mu? Fãce dai dõmin mun yi ĩmãni da Allah da abin da aka Saukar zuwa gare mu da abin da aka saukar daga gabãni, kuma dõmin mafi yawanku fãsiƙai ne."
(60) Ka ce: "Shin, in gaya muku mafi sharri daga wannan, dõmin sakamako daga wurin Allah? wanda Allah Ya la'ane shi kuma Ya yi fushi da shi, kuma Ya sanya daga gare su birai da aladai, kuma ya bauta wa ¦ãguta. Waɗannan ne mafiya sharrin wuri, kuma mafiya ɓata daga tsakar hanya."
(61) Kuma idan sun zo muku sai su ce: "Mun yi ĩmãni." Alhãli kuwa haƙĩƙa, sun shigo da kãfirci, kuma su lalle ne, sun fita da shi, kuma Allah ne Mafi sani ga abin da suka kasance sunã ɓõyewa.
(62) Kuma kana ganin mãsu yawa daga gare su, sunã tseren gaugawa a cikin zunubi da zãlunci da cinsu ga haram. Haƙĩƙa, tir da abin da suka kasance suna aikatãwa.
(63) Don me Malaman Tarbiyya da manyan malamai (na Yahudu) ba su hanã su daga faɗarsu ga zunubi da cinsu ga haram ba? Haƙiƙa, tir daga abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.
(64) Kuma Yahudu suka ce: "Hannun Allah abin yi wa ƙuƙumi ne. " An sanya hannuwansu a cikin ƙuƙumi! Kuma an la'ane su sabõda abin da suka faɗa. Ã'a, hannuwanSa biyu shimfiɗaɗɗu ne, Yanã ciyarwa yadda Yake so. Kuma lalle ne abin da aka saukar zuwa gare ka yanã ƙãra wa mãsu yawa daga gare su, girman kai da kãfirci. Kuma Mun jefa a tsakãninsu, ƙiyayya da ƙeta, zuwa Rãnar ¡iyãma, kõ da yaushe suka hura wata wuta dõmin yãƙi, sai Allah Ya bice ta. Sunã aiki a cikin ƙasa dõmin ɓarna, alhãli kuwa Allah bã Ya son mãsu fasãdi.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022