النجم   سورة  : An-Najm


سورة Sura   النجم   An-Najm
النجم An-Najm
وَالنَّجْمِ إِذَا هَوَىٰ (1) مَا ضَلَّ صَاحِبُكُمْ وَمَا غَوَىٰ (2) وَمَا يَنطِقُ عَنِ الْهَوَىٰ (3) إِنْ هُوَ إِلَّا وَحْيٌ يُوحَىٰ (4) عَلَّمَهُ شَدِيدُ الْقُوَىٰ (5) ذُو مِرَّةٍ فَاسْتَوَىٰ (6) وَهُوَ بِالْأُفُقِ الْأَعْلَىٰ (7) ثُمَّ دَنَا فَتَدَلَّىٰ (8) فَكَانَ قَابَ قَوْسَيْنِ أَوْ أَدْنَىٰ (9) فَأَوْحَىٰ إِلَىٰ عَبْدِهِ مَا أَوْحَىٰ (10) مَا كَذَبَ الْفُؤَادُ مَا رَأَىٰ (11) أَفَتُمَارُونَهُ عَلَىٰ مَا يَرَىٰ (12) وَلَقَدْ رَآهُ نَزْلَةً أُخْرَىٰ (13) عِندَ سِدْرَةِ الْمُنتَهَىٰ (14) عِندَهَا جَنَّةُ الْمَأْوَىٰ (15) إِذْ يَغْشَى السِّدْرَةَ مَا يَغْشَىٰ (16) مَا زَاغَ الْبَصَرُ وَمَا طَغَىٰ (17) لَقَدْ رَأَىٰ مِنْ آيَاتِ رَبِّهِ الْكُبْرَىٰ (18) أَفَرَأَيْتُمُ اللَّاتَ وَالْعُزَّىٰ (19) وَمَنَاةَ الثَّالِثَةَ الْأُخْرَىٰ (20) أَلَكُمُ الذَّكَرُ وَلَهُ الْأُنثَىٰ (21) تِلْكَ إِذًا قِسْمَةٌ ضِيزَىٰ (22) إِنْ هِيَ إِلَّا أَسْمَاءٌ سَمَّيْتُمُوهَا أَنتُمْ وَآبَاؤُكُم مَّا أَنزَلَ اللَّهُ بِهَا مِن سُلْطَانٍ ۚ إِن يَتَّبِعُونَ إِلَّا الظَّنَّ وَمَا تَهْوَى الْأَنفُسُ ۖ وَلَقَدْ جَاءَهُم مِّن رَّبِّهِمُ الْهُدَىٰ (23) أَمْ لِلْإِنسَانِ مَا تَمَنَّىٰ (24) فَلِلَّهِ الْآخِرَةُ وَالْأُولَىٰ (25) ۞ وَكَم مِّن مَّلَكٍ فِي السَّمَاوَاتِ لَا تُغْنِي شَفَاعَتُهُمْ شَيْئًا إِلَّا مِن بَعْدِ أَن يَأْذَنَ اللَّهُ لِمَن يَشَاءُ وَيَرْضَىٰ (26)
الصفحة Page 526
النجم An-Najm
(1) Inã rantsuwa da taurãron, a lõkacin da ya faku.
(2) Ma'abũcinku bai ɓata ba, kuma bai ƙẽtare haddi ba.
(3) Kuma bã ya yin magana daga son zuciyarsa.
(4) (Maganarsa) ba ta zamo ba, fãce wahayi ne da ake aikõwa.
(5) (Malã'ika) mai tsananin ƙarfi ya sanar da shi.
(6) Ma'abũcin ƙarfi da kwarjini, sa'an nan ya daidaita.
(7) Alhãli kuwa yanã a sararin samã mafi aukaka.
(8) Sa'an nan ya kusanta, kuma ya matsa zurõwa.
(9) Har ya kasance gwargwadon zirã'i biyu, kõ kuma abin da ya fi kusa.
(10) Sa'an nan ya yi wahayi zuwa ga bãwan Allah (Muhammadu) da abin da ya faɗa (masa).
(11) Zũciyar (Annabi) bata ƙaryata abin da ya gani ba.
(12) Shin, zã ku yi masa musu a kan abin da yake gani?
(13) Kuma lalle ya gan shi, haƙĩƙatan, a wani lõkacin saukarsa.
(14) A wurin da magaryar tuƙẽwa take.
(15) A inda taken, nan Aljannar makoma take.
(16) Lõkacin da abin da yake rufe magaryar tuƙẽwa ya rufe ta.
(17) Ganinsa bai karkata ba, kuma bai ƙetare haddi ba.
(18) Lalle, tabbas, (Annabinku) ya ga waɗanda suka fi girma daga ãyõyin Ubangijinsa.
(19) Shin, kun ga Lãta da uzza?
(20) Da (wani gunki wai shi) Manãta, na ukunsu?
(21) Ashe, kũ ne da ɗa namiji Shĩ (Allah) kuma da ɗiya mace?
(22) Wannan fa ya zama rabo naƙasasshe.
(23) Waɗannan bã kõme ba ne fãce sũnãye, waɗanda kuka ambace su da su, kũ da uwãyenku. Allah bai saukar da wani dalĩli game da su ba. (Kãfirai) bã su biyar kõme fãce zato da abin da rãyukansu ke so, Alhãli kuwa shiriyar ta daga wajen Ubangijinsu, ta jẽ musu (sai suka bar ta suka kõma wa zaton).
(24) Ko (an fai cẽwa) mutum zai sãmi abin da yake gũri?
(25) To, Lãhira da dũniya na Allah kawai ne (wanda ya nẽme su daga wani, yã yi kuskure).
(26) Akwai malã'iku da yawa a cikin sammai cẽtonsu bã ya wadãtar da kõme fãce bãyan Allah Yã yi izni (da shi) ga wanda Yake so, kuma Yake yarda.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022