القمر   سورة  : Al-Qamar


سورة Sura   القمر   Al-Qamar
وَأَنَّهُ خَلَقَ الزَّوْجَيْنِ الذَّكَرَ وَالْأُنثَىٰ (45) مِن نُّطْفَةٍ إِذَا تُمْنَىٰ (46) وَأَنَّ عَلَيْهِ النَّشْأَةَ الْأُخْرَىٰ (47) وَأَنَّهُ هُوَ أَغْنَىٰ وَأَقْنَىٰ (48) وَأَنَّهُ هُوَ رَبُّ الشِّعْرَىٰ (49) وَأَنَّهُ أَهْلَكَ عَادًا الْأُولَىٰ (50) وَثَمُودَ فَمَا أَبْقَىٰ (51) وَقَوْمَ نُوحٍ مِّن قَبْلُ ۖ إِنَّهُمْ كَانُوا هُمْ أَظْلَمَ وَأَطْغَىٰ (52) وَالْمُؤْتَفِكَةَ أَهْوَىٰ (53) فَغَشَّاهَا مَا غَشَّىٰ (54) فَبِأَيِّ آلَاءِ رَبِّكَ تَتَمَارَىٰ (55) هَٰذَا نَذِيرٌ مِّنَ النُّذُرِ الْأُولَىٰ (56) أَزِفَتِ الْآزِفَةُ (57) لَيْسَ لَهَا مِن دُونِ اللَّهِ كَاشِفَةٌ (58) أَفَمِنْ هَٰذَا الْحَدِيثِ تَعْجَبُونَ (59) وَتَضْحَكُونَ وَلَا تَبْكُونَ (60) وَأَنتُمْ سَامِدُونَ (61) فَاسْجُدُوا لِلَّهِ وَاعْبُدُوا ۩ (62)
القمر Al-Qamar
اقْتَرَبَتِ السَّاعَةُ وَانشَقَّ الْقَمَرُ (1) وَإِن يَرَوْا آيَةً يُعْرِضُوا وَيَقُولُوا سِحْرٌ مُّسْتَمِرٌّ (2) وَكَذَّبُوا وَاتَّبَعُوا أَهْوَاءَهُمْ ۚ وَكُلُّ أَمْرٍ مُّسْتَقِرٌّ (3) وَلَقَدْ جَاءَهُم مِّنَ الْأَنبَاءِ مَا فِيهِ مُزْدَجَرٌ (4) حِكْمَةٌ بَالِغَةٌ ۖ فَمَا تُغْنِ النُّذُرُ (5) فَتَوَلَّ عَنْهُمْ ۘ يَوْمَ يَدْعُ الدَّاعِ إِلَىٰ شَيْءٍ نُّكُرٍ (6)
الصفحة Page 528
(45) Kuma lalle Shĩ ne Ya yi halitta nau'i-nau'i, namiji da mace.
(46) Daga wani ɗigon ruwa guda a lõkacin da ake jẽfa shi a cikin mahaifa.
(47) Kuma a kansa ne ƙãga halitta ta biyu take.
(48) Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya azurta, kuma Ya wadãtar.
(49) Kuma lalle, Shĩ, Shi ne Ubangijin Shi'ira.
(50) Kuma lalle, Shĩ, Shĩ ne Ya halaka Ãdãwa na farko.
(51) Da Samũdãwa, sa'an nan bai rage su ba.
(52) Da mutãnen Nũhu a gabãnin haka, lalle sũ sun kasance mafi zãlunci kuma mafi girman kai.
(53) Da waɗanda aka birkice ƙasarsu, Ya kãyar da su.
(54) Sa'an nan abin da ya rufe su, ya rufe su.
(55) To, da wace daga ni'imõmin Ubangijinka kake yin shakka?
(56) wannan (Muhammadu) mai gargaɗi ne kamar irin mãsu gargaɗi na farko.
(57) Makusanciya fa, tã yi kusa.
(58) Bãbu wani rai, banda Allah, mai iya bãyani gare ta.
(59) Shin, kuma daga wannan lãbãri kuke mãmãki?
(60) Kuma kunã yin dãriya, kuma bã ku yin kũka?
(61) Alhãli kunã mãsu wãsã?
(62) To, ku yi tawãli'u ga Allah, kuma ku bauta (masa).
القمر Al-Qamar
(1) Sã'a ta yi kusa, kuma wata ya tsãge.
(2) Kuma idan sun ga wata ãyã, sai su juya baya su ce: "Sihiri ne mai dõgẽwa!"
(3) Kuma suka ƙaryata, kuma suka bi son zũciyarsu, alhãli kuwa kõwane al'amari (wanda suke son su tũre daga Annabi) an tabbatar da shi.
(4) Kuma lalle, abin da yake akwai tsãwatarwa a cikinsa na lãbãraiya zo musu.
(5) Hikima cikakka! Sai dai abũbuwan gargaɗi bã su amfãni.
(6) Sabõda haka, ka bar su! Rãnar da mai kiran zai yi kira zuwa ga wani abu abin ƙyama.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022