المجادلة   سورة  : Al-Mujaadila


سورة Sura   المجادلة   Al-Mujaadila
أَلَمْ تَرَ أَنَّ اللَّهَ يَعْلَمُ مَا فِي السَّمَاوَاتِ وَمَا فِي الْأَرْضِ ۖ مَا يَكُونُ مِن نَّجْوَىٰ ثَلَاثَةٍ إِلَّا هُوَ رَابِعُهُمْ وَلَا خَمْسَةٍ إِلَّا هُوَ سَادِسُهُمْ وَلَا أَدْنَىٰ مِن ذَٰلِكَ وَلَا أَكْثَرَ إِلَّا هُوَ مَعَهُمْ أَيْنَ مَا كَانُوا ۖ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا عَمِلُوا يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۚ إِنَّ اللَّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ (7) أَلَمْ تَرَ إِلَى الَّذِينَ نُهُوا عَنِ النَّجْوَىٰ ثُمَّ يَعُودُونَ لِمَا نُهُوا عَنْهُ وَيَتَنَاجَوْنَ بِالْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَمَعْصِيَتِ الرَّسُولِ وَإِذَا جَاءُوكَ حَيَّوْكَ بِمَا لَمْ يُحَيِّكَ بِهِ اللَّهُ وَيَقُولُونَ فِي أَنفُسِهِمْ لَوْلَا يُعَذِّبُنَا اللَّهُ بِمَا نَقُولُ ۚ حَسْبُهُمْ جَهَنَّمُ يَصْلَوْنَهَا ۖ فَبِئْسَ الْمَصِيرُ (8) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا تَنَاجَيْتُمْ فَلَا تَتَنَاجَوْا بِالْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ وَمَعْصِيَتِ الرَّسُولِ وَتَنَاجَوْا بِالْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ ۖ وَاتَّقُوا اللَّهَ الَّذِي إِلَيْهِ تُحْشَرُونَ (9) إِنَّمَا النَّجْوَىٰ مِنَ الشَّيْطَانِ لِيَحْزُنَ الَّذِينَ آمَنُوا وَلَيْسَ بِضَارِّهِمْ شَيْئًا إِلَّا بِإِذْنِ اللَّهِ ۚ وَعَلَى اللَّهِ فَلْيَتَوَكَّلِ الْمُؤْمِنُونَ (10) يَا أَيُّهَا الَّذِينَ آمَنُوا إِذَا قِيلَ لَكُمْ تَفَسَّحُوا فِي الْمَجَالِسِ فَافْسَحُوا يَفْسَحِ اللَّهُ لَكُمْ ۖ وَإِذَا قِيلَ انشُزُوا فَانشُزُوا يَرْفَعِ اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ وَالَّذِينَ أُوتُوا الْعِلْمَ دَرَجَاتٍ ۚ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ (11)
الصفحة Page 543
(7) Ashe, ba ka ga cẽwa lalle Allah Yanã sane da abin da yake a cikin sammai da abin da ke cikin ƙasa ba? Wata gãnãwa ta mutum uku bã zã ta kasance ba fãce Allah Shĩ ne na huɗu ɗinta, kuma bãbu ta mutum biyar fãce Shĩ ne na shida ɗinta, kuma babu abin da ya kãsa wannan kuma babu abin da yake mafi yawa fãce Shĩ Yanã tãre da su duk inda suka kasance, sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka aikata a Rãnar ¡iyãma. Lalle Allah Masani ne ga dukkan kõme.
(8) Ashe, ba ka ga waɗanda aka hane su ba daga ganãwar, sa'an nan sunã kõmã wa abin da aka hane su daga gare shi, kuma sunã gãnãwa game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma idan sun zo maka sai su gasihe ka da abin da Allah bai gaishe ka da shi ba, kuma sunã cẽwa a cikin zukatansu: "Don me Allah ba Ya yi mana azãba sabõda abin da muke faɗi?" Jahannama ita ce mai isarsu, zã su shigeta. Sabõda haka makõmarsu ta mũnana.
(9) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan za ku yi gãnãwa, to, kada ku gãna game da zunubi da zãlunci da sãɓã wa Manzon Allah, kuma ku yi gãnãwa game da alhẽri da taƙawa. Ku bi Allah da taƙawa wanda zã a tattara ku zuwa gare, shi.
(10) Gãnãwar daga Shaiɗan take kawai dõmin ya mũnanã wa waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli kuwa bã zai iya cũtar su da kõme ba fãce da iznin Allah. Kuma sai mũminai su dogara ga Allah.
(11) Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Idan an ce muka, "Ku yalwatã a cikin majalisai," to, ku yalwatã, sai Allah Ya yalwatã muku, kuma idan an ce muku, "Ku tãshi" to, ku tãshi. Allah nã ɗaukaka waɗanda suka yi ĩmãni daga cikinku da waɗanda aka bai wa ilim wasu darajõji mãsu yawa, kuma, Allah Mai ƙididdigewa ne ga dukan kõme.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022