الأنعام   سورة  : Al-An'aam


سورة Sura   الأنعام   Al-An'aam
هَلْ يَنظُرُونَ إِلَّا أَن تَأْتِيَهُمُ الْمَلَائِكَةُ أَوْ يَأْتِيَ رَبُّكَ أَوْ يَأْتِيَ بَعْضُ آيَاتِ رَبِّكَ ۗ يَوْمَ يَأْتِي بَعْضُ آيَاتِ رَبِّكَ لَا يَنفَعُ نَفْسًا إِيمَانُهَا لَمْ تَكُنْ آمَنَتْ مِن قَبْلُ أَوْ كَسَبَتْ فِي إِيمَانِهَا خَيْرًا ۗ قُلِ انتَظِرُوا إِنَّا مُنتَظِرُونَ (158) إِنَّ الَّذِينَ فَرَّقُوا دِينَهُمْ وَكَانُوا شِيَعًا لَّسْتَ مِنْهُمْ فِي شَيْءٍ ۚ إِنَّمَا أَمْرُهُمْ إِلَى اللَّهِ ثُمَّ يُنَبِّئُهُم بِمَا كَانُوا يَفْعَلُونَ (159) مَن جَاءَ بِالْحَسَنَةِ فَلَهُ عَشْرُ أَمْثَالِهَا ۖ وَمَن جَاءَ بِالسَّيِّئَةِ فَلَا يُجْزَىٰ إِلَّا مِثْلَهَا وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ (160) قُلْ إِنَّنِي هَدَانِي رَبِّي إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ دِينًا قِيَمًا مِّلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفًا ۚ وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ (161) قُلْ إِنَّ صَلَاتِي وَنُسُكِي وَمَحْيَايَ وَمَمَاتِي لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (162) لَا شَرِيكَ لَهُ ۖ وَبِذَٰلِكَ أُمِرْتُ وَأَنَا أَوَّلُ الْمُسْلِمِينَ (163) قُلْ أَغَيْرَ اللَّهِ أَبْغِي رَبًّا وَهُوَ رَبُّ كُلِّ شَيْءٍ ۚ وَلَا تَكْسِبُ كُلُّ نَفْسٍ إِلَّا عَلَيْهَا ۚ وَلَا تَزِرُ وَازِرَةٌ وِزْرَ أُخْرَىٰ ۚ ثُمَّ إِلَىٰ رَبِّكُم مَّرْجِعُكُمْ فَيُنَبِّئُكُم بِمَا كُنتُمْ فِيهِ تَخْتَلِفُونَ (164) وَهُوَ الَّذِي جَعَلَكُمْ خَلَائِفَ الْأَرْضِ وَرَفَعَ بَعْضَكُمْ فَوْقَ بَعْضٍ دَرَجَاتٍ لِّيَبْلُوَكُمْ فِي مَا آتَاكُمْ ۗ إِنَّ رَبَّكَ سَرِيعُ الْعِقَابِ وَإِنَّهُ لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ (165)
الصفحة Page 150
(158) Shin, sunã jiran (wani abu), fãce dai malã'iku su je musu kõ kuwa Ubangijinka Ya je, kõ kuwa sãshen ãyõyin Ubangijinka ya je. A rãnar da sãshen ãyõyin Ubangijinka yake zuwa, ĩmãnin rai wanda bai kasance yã yi ĩmãnin ba a gabãni, kõ kuwa ya yi tsiwirwirin wani alhẽri, bã ya amfãninsa. Ka ce: "Ku yi jira: Lalle ne mũ, mãsu jira ne."
(159) Lalle ne waɗanda suka rarraba addininsu, kuma suka kasance ƙungiyã-ƙungiyã, kai ba ka zama daga gare su ba, a cikin kõme: abin sani kawai al'amarinsu zuwa ga Allah yake. Sa'an nan Ya bã su lãbãri game da abin da suka kasance sunã aikatãwa.
(160) Wanda ya zo da kyakkyãwan aiki guda, to, yanã da gõma ɗin misãlansa. Kuma wanda ya zo da mũgun aiki gũda, to, bã zã a sãka masa ba fãce da misãlinsa. Kuma sũ bã a zãluntar su.
(161) Ka ce: "Lalle nĩ, Ubangijina Yã shiryar da ni zuwa ga tafarki madaidaici, addĩni, ƙĩmantãwa (ga abũbuwa), mai aƙĩdar Ibrãhĩm, mai karkata zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba."
(162) Ka ce: "Lalle ne sallãta, da baikõna, da rãyuwãta, da mutuwãta, na Allah ne Ubangijin tãlikai."
(163) "Bãbu abõkin tãrayya a gare Shi. Kuma da wancan aka umurce ni, kuma ni ne farkon mãsu sallamãwa."
(164) Ka ce: "Shin wanin Allah nake nẽma ya zama Ubangiji, alhãli kuwa Shĩ ne Ubangijin dukan kõme? Kuma wani rai bã ya yin tsirfa fãce dõmin kansa, kuma mai ɗaukar nauyi, bã ya ɗaukar nauyin wani, sa'an nan kuma kõmawarku zuwa ga Ubangijinku take; Sa'an nan Yã bã ku lãbãri ga abin da kuka kasance, a cikinsa, kunã sãɓã wa jũnã?"
(165) "Kuma Shĩ ne wanda Ya sanya ku mãsu maye wa jũnaga ƙasa. Kuma Ya ɗaukaka sãshenku bisa ga sãshe da darajõji; dõmin Ya jarraba ku a cikin abin da Ya bã ku." Lalle ne, Ubangijinka Mai gaggãwar uƙkũba ne, kuma lalle ne Shi, haƙĩƙa, Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022