الانسان   سورة  : Al-Insaan


سورة Sura   الانسان   Al-Insaan
عَيْنًا يَشْرَبُ بِهَا عِبَادُ اللَّهِ يُفَجِّرُونَهَا تَفْجِيرًا (6) يُوفُونَ بِالنَّذْرِ وَيَخَافُونَ يَوْمًا كَانَ شَرُّهُ مُسْتَطِيرًا (7) وَيُطْعِمُونَ الطَّعَامَ عَلَىٰ حُبِّهِ مِسْكِينًا وَيَتِيمًا وَأَسِيرًا (8) إِنَّمَا نُطْعِمُكُمْ لِوَجْهِ اللَّهِ لَا نُرِيدُ مِنكُمْ جَزَاءً وَلَا شُكُورًا (9) إِنَّا نَخَافُ مِن رَّبِّنَا يَوْمًا عَبُوسًا قَمْطَرِيرًا (10) فَوَقَاهُمُ اللَّهُ شَرَّ ذَٰلِكَ الْيَوْمِ وَلَقَّاهُمْ نَضْرَةً وَسُرُورًا (11) وَجَزَاهُم بِمَا صَبَرُوا جَنَّةً وَحَرِيرًا (12) مُّتَّكِئِينَ فِيهَا عَلَى الْأَرَائِكِ ۖ لَا يَرَوْنَ فِيهَا شَمْسًا وَلَا زَمْهَرِيرًا (13) وَدَانِيَةً عَلَيْهِمْ ظِلَالُهَا وَذُلِّلَتْ قُطُوفُهَا تَذْلِيلًا (14) وَيُطَافُ عَلَيْهِم بِآنِيَةٍ مِّن فِضَّةٍ وَأَكْوَابٍ كَانَتْ قَوَارِيرَا (15) قَوَارِيرَ مِن فِضَّةٍ قَدَّرُوهَا تَقْدِيرًا (16) وَيُسْقَوْنَ فِيهَا كَأْسًا كَانَ مِزَاجُهَا زَنجَبِيلًا (17) عَيْنًا فِيهَا تُسَمَّىٰ سَلْسَبِيلًا (18) ۞ وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ وِلْدَانٌ مُّخَلَّدُونَ إِذَا رَأَيْتَهُمْ حَسِبْتَهُمْ لُؤْلُؤًا مَّنثُورًا (19) وَإِذَا رَأَيْتَ ثَمَّ رَأَيْتَ نَعِيمًا وَمُلْكًا كَبِيرًا (20) عَالِيَهُمْ ثِيَابُ سُندُسٍ خُضْرٌ وَإِسْتَبْرَقٌ ۖ وَحُلُّوا أَسَاوِرَ مِن فِضَّةٍ وَسَقَاهُمْ رَبُّهُمْ شَرَابًا طَهُورًا (21) إِنَّ هَٰذَا كَانَ لَكُمْ جَزَاءً وَكَانَ سَعْيُكُم مَّشْكُورًا (22) إِنَّا نَحْنُ نَزَّلْنَا عَلَيْكَ الْقُرْآنَ تَنزِيلًا (23) فَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ وَلَا تُطِعْ مِنْهُمْ آثِمًا أَوْ كَفُورًا (24) وَاذْكُرِ اسْمَ رَبِّكَ بُكْرَةً وَأَصِيلًا (25)
الصفحة Page 579
(6) Wani marmaro ne, daga gare shi bayin Allah suke sha, suna ɓuɓɓugar da shi ɓuɓɓugarwa.
(7) Suna cikãwa da alwãshin (da suka bãkanta), kuma suna tsõron wani yini wanda sharrinsa ya kasance mai tartsatsi ne.
(8) Kuma suna ciyar da abinci, a kan suna bukãtarsa, ga matalauci da marãya da kãmamme.
(9) (Suna cẽwa): "Munã ciyar da ku ne dõmin nẽman yardar Allah kawai, bã mu nufin sãmun wani sakamako daga gare ku, kuma bã mu nufin gõdiya.
(10) "Lalle ne, mũ muna tsõro daga Ubangijinmu, wani yini mai gintsẽwa, mai murtukẽwa."
(11) Sabõda haka Allah Ya tsare musu sharrin wannan yini, kuma Ya hlɗa su da annũrin huska da farin ciki,
(12) Kuma Ya sãka musu sabõda haƙurin da suka yi, da Aljanna da tufãfin alharini.
(13) Sunã mãsu zaman ginciri, a cikinta, a kan karagu, bã su ganin rãnã a cikinta, kuma bã su ganin jaura.
(14) Kuma, inuwõyinta suna kusa, a kansu, an hõre nunannun 'yã'yan itãcenta, hõrẽwa.
(15) Kuma ana kẽwayãwa a kansu da finjãlai na azurfa da kofuna waɗanda suka kasance na ƙarau.
(16) ¡arau na azurfa, sun ƙaddara su ƙaddarawa, daidai bukãta.
(17) Ana shayarwa da su, a cikinta, finjalan giya, wadda abin gaurayarta ya kasance zanjabil ne.
(18) Wani marmaro ne, a cikinta, ana kiran sa salsabil.
(19) Kuma wasu yara samãrin dindindin na kẽwayãwa, a kansu, idan ka gan su, zã ka zaci sũ lu'ulu'u ne wanda aka wãtsa.
(20) Kuma idan kã ga wannan wurin, to, kã ga wata irin ni'ima da mulki babba.
(21) Tufãfinsu na sama na alharĩ ni ne, kõre da mai walƙiya, kuma an ƙawãce su da mundãye na wata curin azurfa kuma Ubangijinsu, Ya shãyar da su abin sha mai tsarkakẽwar (ciki).
(22) (A ce musu) "Lalle ne, wannan ya kasance, a gare ku sakamako, kuma aikink. ya kasance abin gõdewa."
(23) Lalle, Mũ ne Muka saukar da Alƙur'ãni a gare ka, saukarwa.
(24) Sabõda haka ka yi haƙuri ga hukuncin Ubangijinka, kuma kada ka bi, daga cikinsu, mai zunubi ko mai kãfirci.
(25) Kuma ka ambaci sũnan Ubangijinka, sãfe da maraice.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022