النحل   سورة  : An-Nahl


سورة Sura   النحل   An-Nahl
۞ يَوْمَ تَأْتِي كُلُّ نَفْسٍ تُجَادِلُ عَن نَّفْسِهَا وَتُوَفَّىٰ كُلُّ نَفْسٍ مَّا عَمِلَتْ وَهُمْ لَا يُظْلَمُونَ (111) وَضَرَبَ اللَّهُ مَثَلًا قَرْيَةً كَانَتْ آمِنَةً مُّطْمَئِنَّةً يَأْتِيهَا رِزْقُهَا رَغَدًا مِّن كُلِّ مَكَانٍ فَكَفَرَتْ بِأَنْعُمِ اللَّهِ فَأَذَاقَهَا اللَّهُ لِبَاسَ الْجُوعِ وَالْخَوْفِ بِمَا كَانُوا يَصْنَعُونَ (112) وَلَقَدْ جَاءَهُمْ رَسُولٌ مِّنْهُمْ فَكَذَّبُوهُ فَأَخَذَهُمُ الْعَذَابُ وَهُمْ ظَالِمُونَ (113) فَكُلُوا مِمَّا رَزَقَكُمُ اللَّهُ حَلَالًا طَيِّبًا وَاشْكُرُوا نِعْمَتَ اللَّهِ إِن كُنتُمْ إِيَّاهُ تَعْبُدُونَ (114) إِنَّمَا حَرَّمَ عَلَيْكُمُ الْمَيْتَةَ وَالدَّمَ وَلَحْمَ الْخِنزِيرِ وَمَا أُهِلَّ لِغَيْرِ اللَّهِ بِهِ ۖ فَمَنِ اضْطُرَّ غَيْرَ بَاغٍ وَلَا عَادٍ فَإِنَّ اللَّهَ غَفُورٌ رَّحِيمٌ (115) وَلَا تَقُولُوا لِمَا تَصِفُ أَلْسِنَتُكُمُ الْكَذِبَ هَٰذَا حَلَالٌ وَهَٰذَا حَرَامٌ لِّتَفْتَرُوا عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ ۚ إِنَّ الَّذِينَ يَفْتَرُونَ عَلَى اللَّهِ الْكَذِبَ لَا يُفْلِحُونَ (116) مَتَاعٌ قَلِيلٌ وَلَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ (117) وَعَلَى الَّذِينَ هَادُوا حَرَّمْنَا مَا قَصَصْنَا عَلَيْكَ مِن قَبْلُ ۖ وَمَا ظَلَمْنَاهُمْ وَلَٰكِن كَانُوا أَنفُسَهُمْ يَظْلِمُونَ (118)
الصفحة Page 280
(111) A rãnar da kõwane rai zai je yanã jãyayyar tunkuɗẽwa daga kansa, kuma a cika wa kõwane rai (sakamakon) abin da ya aikata, kuma sũ bã zã a zãlunce su ba.
(112) Kuma Allah Ya buga misãli, wata alƙarya ta kasance amintacciyã, natsattsiyã, arzikinta yanã je mata a wadãce daga kõwane wuri sai ta kãfirta da ni'imõmin Allah, sabõda haka Allah ya ɗanɗana mata tufãfin yunwa da tsõro, sabõda abin da suka kasance sunã sanã'antãwa.
(113) Kuma lalle ne haƙĩƙa wani Manzo daga gare su, ya jẽmusu, sai suka ƙaryata shi, sabõda haka azãba ta kãma su, alhãli kuwa sũ ne mãsu zãlunci.
(114) Sa'an nan ku ci daga abin da Allah Ya azurta ku da shi, halas, kuma mai dãɗi, kuma ku gõde wa ni'imar Allah idan kun kasance shi kuke bautãwa.
(115) Abin sani kawai (Allah) Ya haramta muku mussai da jini da nãman alade da abin da aka ambaci sũnan wanin Allah game da shi. Sa'an nan wanda aka tĩlastaa kan jama'a kuma baicin mai zãlunci, to, lalle Allah ne Mai gãfara, Mai jin ƙai.
(116) Kuma kada ku ce, dõmin abin da harsunanku suke siffantawa da ƙarya, "Wannan halas ne, kuma wannan harãmun ne." Dõmin ku ƙirƙira ƙarya ga Allah. Lalle ne, waɗanda suke ƙirƙira ƙarya ga Allah bã zã su ci nasara ba.
(117) Jin dãɗi ne kaɗan. Kuma sunã da wata azãba mai raɗaɗi.
(118) Kuma kan waɗanda suka tũba (Yãhũdu) Mun haramta abin da Muka bãyar da lãbari a gare ka daga gabãni, kuma ba Mu zãlunce su ba, amma sun kasance kansu suke zãlunta.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022