النحل   سورة  : An-Nahl


سورة Sura   النحل   An-Nahl
ثُمَّ إِنَّ رَبَّكَ لِلَّذِينَ عَمِلُوا السُّوءَ بِجَهَالَةٍ ثُمَّ تَابُوا مِن بَعْدِ ذَٰلِكَ وَأَصْلَحُوا إِنَّ رَبَّكَ مِن بَعْدِهَا لَغَفُورٌ رَّحِيمٌ (119) إِنَّ إِبْرَاهِيمَ كَانَ أُمَّةً قَانِتًا لِّلَّهِ حَنِيفًا وَلَمْ يَكُ مِنَ الْمُشْرِكِينَ (120) شَاكِرًا لِّأَنْعُمِهِ ۚ اجْتَبَاهُ وَهَدَاهُ إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ (121) وَآتَيْنَاهُ فِي الدُّنْيَا حَسَنَةً ۖ وَإِنَّهُ فِي الْآخِرَةِ لَمِنَ الصَّالِحِينَ (122) ثُمَّ أَوْحَيْنَا إِلَيْكَ أَنِ اتَّبِعْ مِلَّةَ إِبْرَاهِيمَ حَنِيفًا ۖ وَمَا كَانَ مِنَ الْمُشْرِكِينَ (123) إِنَّمَا جُعِلَ السَّبْتُ عَلَى الَّذِينَ اخْتَلَفُوا فِيهِ ۚ وَإِنَّ رَبَّكَ لَيَحْكُمُ بَيْنَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ فِيمَا كَانُوا فِيهِ يَخْتَلِفُونَ (124) ادْعُ إِلَىٰ سَبِيلِ رَبِّكَ بِالْحِكْمَةِ وَالْمَوْعِظَةِ الْحَسَنَةِ ۖ وَجَادِلْهُم بِالَّتِي هِيَ أَحْسَنُ ۚ إِنَّ رَبَّكَ هُوَ أَعْلَمُ بِمَن ضَلَّ عَن سَبِيلِهِ ۖ وَهُوَ أَعْلَمُ بِالْمُهْتَدِينَ (125) وَإِنْ عَاقَبْتُمْ فَعَاقِبُوا بِمِثْلِ مَا عُوقِبْتُم بِهِ ۖ وَلَئِن صَبَرْتُمْ لَهُوَ خَيْرٌ لِّلصَّابِرِينَ (126) وَاصْبِرْ وَمَا صَبْرُكَ إِلَّا بِاللَّهِ ۚ وَلَا تَحْزَنْ عَلَيْهِمْ وَلَا تَكُ فِي ضَيْقٍ مِّمَّا يَمْكُرُونَ (127) إِنَّ اللَّهَ مَعَ الَّذِينَ اتَّقَوا وَّالَّذِينَ هُم مُّحْسِنُونَ (128)
الصفحة Page 281
(119) Sa'an nan kuma lalle ne Ubangijinka ga waɗanda suka aikata mummunan aiki da jãhilci, sa'an nan suka tũba daga bãyan wancan, kuma suka gyãra, lalle ne Ubangijinka, daga bãyanta haƙĩƙa Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
(120) Lalle ne Ibrãhĩm ya kasance shũgaba, mai ƙasƙantar da kai ga Allah, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.
(121) Mai gõdiya ga ni'imominSa (Allah), Ya zãɓe shi, kuma Ya shiryar da shi zuwa ga tafarki madaidaici.
(122) Kuma Muka ba shi alhẽri a cikin dũniya, Kuma lalle shĩ, a Lãhira, yanã daga sãlihai.
(123) Sa'an nan kuma Muka yi wahayi zuwa gare ka (cẽwa), "Ka bi aƙĩdar Ibrahĩm, mai karkatã zuwa ga gaskiya, kuma bai kasance daga mãsu shirki ba.'
(124) Abin sani kawai, an sanya Asabar a kan waɗanda suka sãɓã wajũna a cikin sha'aninsa. Kuma lalle ne Ubangijinka, haƙĩƙa, Yanã yin hukunci a tsakaninsu a Rãnar ¡iyãma a cikin abin da suka kasance a cikinsa sunã sãɓã wa jũnã.
(125) Ka yi kira zuwa ga hanyar Ubangijinka da hikima da wa'azi mai kyau kuma ka yi jãyayya da su da magana wadda take mafi kyau. Lalle ne Ubangijinka Shĩ neMafi sani ga wanda ya ɓãce daga hanyarSa, kuma Shi ne Mafi sani ga mãsu shiryuwa.
(126) Kuma idan kuka sãka wa uƙũba to ku sãka wa uƙũba da misãlin abin da aka yi muku uƙũbar da shi. Kuma idan kun yi haƙuri, lalle shĩ ne mafi alhẽri ga mãsu haƙuri.
(127) Kuma ka yi haƙuri, kuma haƙurinka bã zai zama ba fãce dõmin Allah, kuma kada ka yi baƙin ciki sabo da su, kuma kada ka kasance a cikin ƙuncin rai daga abin da suke yi na mãkirci.
(128) Lalle Allah Yanã tãre da waɗanda suka yi taƙawa da waɗanda suke sũ mãsu kyautatãwa ne.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022