الروم   سورة  : Ar-Room


سورة Sura   الروم   Ar-Room
وَأَمَّا الَّذِينَ كَفَرُوا وَكَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَلِقَاءِ الْآخِرَةِ فَأُولَٰئِكَ فِي الْعَذَابِ مُحْضَرُونَ (16) فَسُبْحَانَ اللَّهِ حِينَ تُمْسُونَ وَحِينَ تُصْبِحُونَ (17) وَلَهُ الْحَمْدُ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَعَشِيًّا وَحِينَ تُظْهِرُونَ (18) يُخْرِجُ الْحَيَّ مِنَ الْمَيِّتِ وَيُخْرِجُ الْمَيِّتَ مِنَ الْحَيِّ وَيُحْيِي الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ وَكَذَٰلِكَ تُخْرَجُونَ (19) وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَكُم مِّن تُرَابٍ ثُمَّ إِذَا أَنتُم بَشَرٌ تَنتَشِرُونَ (20) وَمِنْ آيَاتِهِ أَنْ خَلَقَ لَكُم مِّنْ أَنفُسِكُمْ أَزْوَاجًا لِّتَسْكُنُوا إِلَيْهَا وَجَعَلَ بَيْنَكُم مَّوَدَّةً وَرَحْمَةً ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَتَفَكَّرُونَ (21) وَمِنْ آيَاتِهِ خَلْقُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ وَاخْتِلَافُ أَلْسِنَتِكُمْ وَأَلْوَانِكُمْ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّلْعَالِمِينَ (22) وَمِنْ آيَاتِهِ مَنَامُكُم بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ وَابْتِغَاؤُكُم مِّن فَضْلِهِ ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَسْمَعُونَ (23) وَمِنْ آيَاتِهِ يُرِيكُمُ الْبَرْقَ خَوْفًا وَطَمَعًا وَيُنَزِّلُ مِنَ السَّمَاءِ مَاءً فَيُحْيِي بِهِ الْأَرْضَ بَعْدَ مَوْتِهَا ۚ إِنَّ فِي ذَٰلِكَ لَآيَاتٍ لِّقَوْمٍ يَعْقِلُونَ (24)
الصفحة Page 406
(16) Kuma waɗanda suka kãfirta, kuma suka ƙaryata, game da ãyõyinMu da kuma haɗuwa da Rãnar Lãhira, to, waɗancan anã halartar da su a cikin azãba.
(17) Sabõda haka tsarkakẽwa ta tabbata ga Allah a lõkacin da kuke shiga maraice, da lõkacin da kuke shiga sãfiya.
(18) Kuma Shĩ ne da gõdiya, a cikin sammai da ƙasã kuma da lõkacin yamma da lõkacin zawãli.
(19) Yanã fitar da mai rai daga matacce kuma Yanã fitar da matacce daga mai rai, kuma Yanã rãyar da ƙasa a bãyan mutuwarta. Kuma haka ake fitar da ku.
(20) Kuma akwai daga ãyõyinSa, Ya halitta ku daga turɓãya, sai gã ku kun zama mutum, kunã wãtsuwa.
(21) Kuma akwai daga ãyõyinsa, Ya halitta muku mãtan aure daga kanku, dõmin ku natsu zuwa gare ta, kuma Ya sanya sõyayya da rahama a tsakãninku. Lalle a cikin wancan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu yin tunãni.
(22) Kuma akwai daga ãyõyinSa halittar sammai da ƙasã da sãɓã, war harsunanku, da launukanku. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mãsu ilmi.
(23) Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, barcinku a cikin dare da rãna, da nẽmanku ga falalarsa. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu saurãrãwa.
(24) Kuma akwai daga cikin ãyõyinSa, Ya nũna muku walƙiya a kan tsõro da ɗammãni kuma Ya dinga saukar da ruwa daga sama Sa'an nan Ya rãyar da ƙasã game da shi a bãyan mutuwarta. Lalle a cikin wannan akwai ãyõyi ga mutãne mãsu hankaltawa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022