الروم   سورة  : Ar-Room


سورة Sura   الروم   Ar-Room
وَمِنْ آيَاتِهِ أَن تَقُومَ السَّمَاءُ وَالْأَرْضُ بِأَمْرِهِ ۚ ثُمَّ إِذَا دَعَاكُمْ دَعْوَةً مِّنَ الْأَرْضِ إِذَا أَنتُمْ تَخْرُجُونَ (25) وَلَهُ مَن فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ كُلٌّ لَّهُ قَانِتُونَ (26) وَهُوَ الَّذِي يَبْدَأُ الْخَلْقَ ثُمَّ يُعِيدُهُ وَهُوَ أَهْوَنُ عَلَيْهِ ۚ وَلَهُ الْمَثَلُ الْأَعْلَىٰ فِي السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۚ وَهُوَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (27) ضَرَبَ لَكُم مَّثَلًا مِّنْ أَنفُسِكُمْ ۖ هَل لَّكُم مِّن مَّا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُم مِّن شُرَكَاءَ فِي مَا رَزَقْنَاكُمْ فَأَنتُمْ فِيهِ سَوَاءٌ تَخَافُونَهُمْ كَخِيفَتِكُمْ أَنفُسَكُمْ ۚ كَذَٰلِكَ نُفَصِّلُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْقِلُونَ (28) بَلِ اتَّبَعَ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَهْوَاءَهُم بِغَيْرِ عِلْمٍ ۖ فَمَن يَهْدِي مَنْ أَضَلَّ اللَّهُ ۖ وَمَا لَهُم مِّن نَّاصِرِينَ (29) فَأَقِمْ وَجْهَكَ لِلدِّينِ حَنِيفًا ۚ فِطْرَتَ اللَّهِ الَّتِي فَطَرَ النَّاسَ عَلَيْهَا ۚ لَا تَبْدِيلَ لِخَلْقِ اللَّهِ ۚ ذَٰلِكَ الدِّينُ الْقَيِّمُ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ (30) ۞ مُنِيبِينَ إِلَيْهِ وَاتَّقُوهُ وَأَقِيمُوا الصَّلَاةَ وَلَا تَكُونُوا مِنَ الْمُشْرِكِينَ (31) مِنَ الَّذِينَ فَرَّقُوا دِينَهُمْ وَكَانُوا شِيَعًا ۖ كُلُّ حِزْبٍ بِمَا لَدَيْهِمْ فَرِحُونَ (32)
الصفحة Page 407
(25) Kuma akwai daga ãyõyinsa, tsayuwar sama da asƙã bisa umurninsa, sa'an nan idan Ya kira ku, kira ɗaya, daga ƙasã, sai gã ku kunã fita.
(26) Kuma wanda ke cikin sammai da ƙasã Nãsa ne shi kaɗai. Dukansu mãsu tawãli'u ne a gare Shi.
(27) Kuma Shĩ ne Wanda Ya fãra halitta, sa'an nan Ya sãke ta kuma sakẽwarta tã fi sauƙi a gare shi. Kuma Yanã da misãli wanda ya fi ɗaukaka a cikin sammai da ƙasã kuma Shĩ ne Mabuwãyi, Mai jin ƙai.
(28) Ya bũga muku wani misãli daga kanku. Kõ kunã da abõkan tarẽwa, daga cikin bãyin da hannãyenku na dãma suka mallaka, a cikin arzikinku, watau ku zama daidai a ciki kunã tsõron su kamar tSõronku ga kanku? Haka dai Muke bayyana ãyõyi, daki-daki, ga mutãne mãsu hankaltawa.
(29) Ã'aha! waɗanda suka yi zã1unci sun bi son zũciyõyinsu, bã tãre da wani ilmi ba. To wãne ne zai shiryar da wanda Allah Ya ɓatar, kuma bã su da waɗansu mataimaka?
(30) Sabõda haka, ka tsayar da fuskarka ga addini, kanã mai karkata zuwa ga gaskiya, halittar Allah da Ya halitta mutãne a kanta. Bãbu musanyãwa ga halittar Allah, wannan shĩ ne addini madaidaici kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
(31) Kunã mãsu mai da al'amari gare Shi, kuma ku bĩ Shi dataƙawa, kuma ku tsayar da salla, kuma kada ku kasance daga mushirikai.
(32) Wãtau waɗanda suka rarrabe addininsu kuma suka kasance ƙungiya-ƙungiya, kõwace ƙungiya tanã mai farin ciki da abin da ke a gare ta kawai.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022