سبإ   سورة  : Saba


سورة Sura   سبإ   Saba
وَلَا تَنفَعُ الشَّفَاعَةُ عِندَهُ إِلَّا لِمَنْ أَذِنَ لَهُ ۚ حَتَّىٰ إِذَا فُزِّعَ عَن قُلُوبِهِمْ قَالُوا مَاذَا قَالَ رَبُّكُمْ ۖ قَالُوا الْحَقَّ ۖ وَهُوَ الْعَلِيُّ الْكَبِيرُ (23) ۞ قُلْ مَن يَرْزُقُكُم مِّنَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ قُلِ اللَّهُ ۖ وَإِنَّا أَوْ إِيَّاكُمْ لَعَلَىٰ هُدًى أَوْ فِي ضَلَالٍ مُّبِينٍ (24) قُل لَّا تُسْأَلُونَ عَمَّا أَجْرَمْنَا وَلَا نُسْأَلُ عَمَّا تَعْمَلُونَ (25) قُلْ يَجْمَعُ بَيْنَنَا رَبُّنَا ثُمَّ يَفْتَحُ بَيْنَنَا بِالْحَقِّ وَهُوَ الْفَتَّاحُ الْعَلِيمُ (26) قُلْ أَرُونِيَ الَّذِينَ أَلْحَقْتُم بِهِ شُرَكَاءَ ۖ كَلَّا ۚ بَلْ هُوَ اللَّهُ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ (27) وَمَا أَرْسَلْنَاكَ إِلَّا كَافَّةً لِّلنَّاسِ بَشِيرًا وَنَذِيرًا وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَ النَّاسِ لَا يَعْلَمُونَ (28) وَيَقُولُونَ مَتَىٰ هَٰذَا الْوَعْدُ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (29) قُل لَّكُم مِّيعَادُ يَوْمٍ لَّا تَسْتَأْخِرُونَ عَنْهُ سَاعَةً وَلَا تَسْتَقْدِمُونَ (30) وَقَالَ الَّذِينَ كَفَرُوا لَن نُّؤْمِنَ بِهَٰذَا الْقُرْآنِ وَلَا بِالَّذِي بَيْنَ يَدَيْهِ ۗ وَلَوْ تَرَىٰ إِذِ الظَّالِمُونَ مَوْقُوفُونَ عِندَ رَبِّهِمْ يَرْجِعُ بَعْضُهُمْ إِلَىٰ بَعْضٍ الْقَوْلَ يَقُولُ الَّذِينَ اسْتُضْعِفُوا لِلَّذِينَ اسْتَكْبَرُوا لَوْلَا أَنتُمْ لَكُنَّا مُؤْمِنِينَ (31)
الصفحة Page 431
(23) "Kuma wani cẽto bã ya amfãni a wurinSa face fa ga wanda Ya yi izni a gare shi. Har a lõkacin da aka kuranye tsõro daga zukãtansu, sai su ce, 'Mẽne ne Ubangijinku Ya ce?' Suka ce: 'Gaskiya', kuma shi ne Maɗaukaki, Mai girma,"
(24) Ka ce: "Wãne ne yake azurta ku daga sama da ƙasa?" Ka ce: "Allah kuma lalle mũ kõ ku, wani yanã a kan shiriya, kõ yana a cikin ɓata bayyananniya."
(25) Ka ce: "Bã zã a tambaye ku ba ga abin da muka aikata daga laifi, kuma bã zã a tambaye mu daga abin da kuke aikatawa ba."
(26) Ka ce: "Ubangijinmu zai tãra tsakãninmu, sa'an nan Ya yi hukunci a tsakaninmu da gaskiya. Kuma Shĩ ne Mahukunci, Masani."
(27) Ka ce: "Ku nũna mini waɗanda kuka riskar da Shi, su zama abõkan tãrayya. Ã'a, Shĩ ne Allah, Mabuwãyi, Mai hikima."
(28) Kuma ba Mu aika ka ba fãce zuwa ga mutãne gabã ɗaya, kanã mai bãyar da bushãra kuma mai gargaɗi, kuma amma mafi yawan mutãne ba su sani ba.
(29) Sunã cẽwa, "Yaushe ne wannan wa'adi zai auku idan kun kasance mãsu gaskiya?"
(30) Ka ce: "Kunã da mi'ãdin wani yini wanda bã ku jinkirta daga gare shi kõ da sa'a ɗaya, kuma bã ku gabãta."
(31) Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Bã zã mu yi ĩmanida wannan Alƙur'ãni ba, kuma bã zã mu yi ĩmani da abin da yakea gabãninsa ba (na waɗansu littattafan sama)." Kuma dã kã gani a lõkacin da azzãlumai suke abin tsayarwa wurin Ubangijinka, sashensu na mayar wa sãshe maganar maraunana (mabiya) suke cẽwa makangara (shũgabanni) "Ba dõminku ba, lalle, dã mun kasance mũminai."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022