سبإ Saba
(1) Gõdiya ta tabbata ga Allah, wanda Yake abin da yake a cikin sammai da abin da yake a cikin ƙasã Nãsa ne, kuma shĩ ne Mai hikima, Mai labartawa.
(2) Yã san abin da yake shiga a cikin ƙasã da abin da yake fita daga gare ta, da abin da yake sauka daga sama da abin da yake hawa a cikinta, kuma Shĩ ne Mai jin ƙai, Mai gãfara.
(3) Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Sã'a bã zã ta zo mana ba." Ka ce: "Kayya! Na rantse da Ubangijĩna, lalle, zã ta zõ muku." Masanin gaibi, gwargwadon zarra bã ta nĩsanta daga gare Shi a cikin sammai kuma bã ta nĩsanta a cikin ƙasã, kuma bãbu mafi ƙaranci daga wancan kuma bãbu mafi girma fãce yanã a cikin Littãfi bayyananne.
(4) Dõmin Ya sãkã wa waɗanda suka yi ĩmãni kuma suka aikata ayyukan ƙwarai. Waɗancan suna da wata gãfara da wani arziki mai karimci.
(5) Kuma waɗanda suka yi mãkirci ga ãyõyinMu, sunã mãsu gajiyarwa, waɗannan sunã da wata azãba daga azãba mai raɗaɗi.
(6) Kuma waɗanda aka bai wa ilmi sunã ganin abin nan da aka saukar zuwa gare ka daga Ubangijinka, shi ne gaskiya, kuma yanã shiryarwa zuwa ga hanyar Mabuwãyi, Gõdadde.
(7) Kuma waɗanda suka kãfirta suka ce: "Shin zã mu nũna muku wani namiji wanda yake gaya muku wai idan an tsattsãge ku, kõwace irin tsattsãgẽwa, lalle kũ, tabbas, kunã a cikin wata halitta sãbuwa.?"