الطور   سورة  : At-Tur


سورة Sura   الطور   At-Tur
أَفَسِحْرٌ هَٰذَا أَمْ أَنتُمْ لَا تُبْصِرُونَ (15) اصْلَوْهَا فَاصْبِرُوا أَوْ لَا تَصْبِرُوا سَوَاءٌ عَلَيْكُمْ ۖ إِنَّمَا تُجْزَوْنَ مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (16) إِنَّ الْمُتَّقِينَ فِي جَنَّاتٍ وَنَعِيمٍ (17) فَاكِهِينَ بِمَا آتَاهُمْ رَبُّهُمْ وَوَقَاهُمْ رَبُّهُمْ عَذَابَ الْجَحِيمِ (18) كُلُوا وَاشْرَبُوا هَنِيئًا بِمَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (19) مُتَّكِئِينَ عَلَىٰ سُرُرٍ مَّصْفُوفَةٍ ۖ وَزَوَّجْنَاهُم بِحُورٍ عِينٍ (20) وَالَّذِينَ آمَنُوا وَاتَّبَعَتْهُمْ ذُرِّيَّتُهُم بِإِيمَانٍ أَلْحَقْنَا بِهِمْ ذُرِّيَّتَهُمْ وَمَا أَلَتْنَاهُم مِّنْ عَمَلِهِم مِّن شَيْءٍ ۚ كُلُّ امْرِئٍ بِمَا كَسَبَ رَهِينٌ (21) وَأَمْدَدْنَاهُم بِفَاكِهَةٍ وَلَحْمٍ مِّمَّا يَشْتَهُونَ (22) يَتَنَازَعُونَ فِيهَا كَأْسًا لَّا لَغْوٌ فِيهَا وَلَا تَأْثِيمٌ (23) ۞ وَيَطُوفُ عَلَيْهِمْ غِلْمَانٌ لَّهُمْ كَأَنَّهُمْ لُؤْلُؤٌ مَّكْنُونٌ (24) وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ (25) قَالُوا إِنَّا كُنَّا قَبْلُ فِي أَهْلِنَا مُشْفِقِينَ (26) فَمَنَّ اللَّهُ عَلَيْنَا وَوَقَانَا عَذَابَ السَّمُومِ (27) إِنَّا كُنَّا مِن قَبْلُ نَدْعُوهُ ۖ إِنَّهُ هُوَ الْبَرُّ الرَّحِيمُ (28) فَذَكِّرْ فَمَا أَنتَ بِنِعْمَتِ رَبِّكَ بِكَاهِنٍ وَلَا مَجْنُونٍ (29) أَمْ يَقُولُونَ شَاعِرٌ نَّتَرَبَّصُ بِهِ رَيْبَ الْمَنُونِ (30) قُلْ تَرَبَّصُوا فَإِنِّي مَعَكُم مِّنَ الْمُتَرَبِّصِينَ (31)
الصفحة Page 524
(15) "To, shin wannan sihiri ne kõ kuwa kũ ne bã ku gani?"
(16) "Ku shigẽ ta. To, ku yi haƙuri ko kuma kada ku yi haƙuri, dai dai ne a kanku, kawai anã yi muku sakamakon abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
(17) Lalle, mãsu taƙawa, sunã a cikin gidãjen Aljanna da wata ni'ima.
(18) Sunã mãsu jin dãɗi da abin da Ubangijinsu Ya ba su, kuma Ubangijinsu Ya tsãre musu azãbar Jahĩm.
(19) (A ce musu): "Ku ci, ku sha, da ni'ima, dõmin abin da kuka kasance kunã aikatãwa."
(20) Sunã kishingiɗe a kan karagu waɗanda ke cikin sahu, kuma Muka aurar da su waɗansu mãtã mãsu farin idãnu, mãsu girmansu.
(21) Kuma waɗanda suka yi ĩmãni kuma zũriyarsu suka bĩ su ga ĩmãnin, Mun riskar da zũriyarsu da su, alhãli kuwa bã da Mun rage musu kõme ba daga aikinsu, kõwane mutum jingina ne ga abin da ya sana'anta.
(22) Kuma Muka yalwata musu 'ya'yan itãce da nãma irin wanda suke marmari.
(23) Sunã mĩƙa wa jũnansu a cikinta hinjãlan giya, wadda bãbu yãsassar magana a cikinta, kuma bãbu jin nauyin zunubi.
(24) Kuma waɗansu samãri nã gẽwayãwa a kansu, kamar dai sũ lu'ulu'u ne wanda ke kulle.
(25) Waɗansunsu suka fuskanta zuwa ga waɗansu, sunã tambayar jũna.
(26) Suka ce: "Lalle mũ mun kasance a gabãnin wannan (a dũniya) a cikin iyãlanmu munã jin tsõro."
(27) "To, Allah Yã yi mana kyautar falala, kuma Yã tsare mana azãbar iskar zãfi."
(28) "Lalle mũ mun kasance, a gãbanin haka, munã kiran sa. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai kyautatãwa, Mai rahama."
(29) To, ka tunãtar kai fa sabõda ni'imar Ubangjinka, bã bõka kake ba, kuma bã mahaukaci ba.
(30) Shin zã su ce: "Mawãƙi ne, munã jiran, masĩfun mutuwa game da shĩ"?
(31) Ka ce: "Ku yi jira, domin nĩ ma lalle inã a cikin mãsu jira tãre da ku."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022