الطور   سورة  : At-Tur


سورة Sura   الطور   At-Tur
أَمْ تَأْمُرُهُمْ أَحْلَامُهُم بِهَٰذَا ۚ أَمْ هُمْ قَوْمٌ طَاغُونَ (32) أَمْ يَقُولُونَ تَقَوَّلَهُ ۚ بَل لَّا يُؤْمِنُونَ (33) فَلْيَأْتُوا بِحَدِيثٍ مِّثْلِهِ إِن كَانُوا صَادِقِينَ (34) أَمْ خُلِقُوا مِنْ غَيْرِ شَيْءٍ أَمْ هُمُ الْخَالِقُونَ (35) أَمْ خَلَقُوا السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ ۚ بَل لَّا يُوقِنُونَ (36) أَمْ عِندَهُمْ خَزَائِنُ رَبِّكَ أَمْ هُمُ الْمُصَيْطِرُونَ (37) أَمْ لَهُمْ سُلَّمٌ يَسْتَمِعُونَ فِيهِ ۖ فَلْيَأْتِ مُسْتَمِعُهُم بِسُلْطَانٍ مُّبِينٍ (38) أَمْ لَهُ الْبَنَاتُ وَلَكُمُ الْبَنُونَ (39) أَمْ تَسْأَلُهُمْ أَجْرًا فَهُم مِّن مَّغْرَمٍ مُّثْقَلُونَ (40) أَمْ عِندَهُمُ الْغَيْبُ فَهُمْ يَكْتُبُونَ (41) أَمْ يُرِيدُونَ كَيْدًا ۖ فَالَّذِينَ كَفَرُوا هُمُ الْمَكِيدُونَ (42) أَمْ لَهُمْ إِلَٰهٌ غَيْرُ اللَّهِ ۚ سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يُشْرِكُونَ (43) وَإِن يَرَوْا كِسْفًا مِّنَ السَّمَاءِ سَاقِطًا يَقُولُوا سَحَابٌ مَّرْكُومٌ (44) فَذَرْهُمْ حَتَّىٰ يُلَاقُوا يَوْمَهُمُ الَّذِي فِيهِ يُصْعَقُونَ (45) يَوْمَ لَا يُغْنِي عَنْهُمْ كَيْدُهُمْ شَيْئًا وَلَا هُمْ يُنصَرُونَ (46) وَإِنَّ لِلَّذِينَ ظَلَمُوا عَذَابًا دُونَ ذَٰلِكَ وَلَٰكِنَّ أَكْثَرَهُمْ لَا يَعْلَمُونَ (47) وَاصْبِرْ لِحُكْمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعْيُنِنَا ۖ وَسَبِّحْ بِحَمْدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ (48) وَمِنَ اللَّيْلِ فَسَبِّحْهُ وَإِدْبَارَ النُّجُومِ (49)
الصفحة Page 525
(32) Shin, hankulansu ne ke umarin su da wannan, kõ kuwa sũ wasu mutãne ne mãsu ƙetare haddi?
(33) Shin, cẽwa suke yi: "Shi ne ke ƙãga faɗarsa"? Ã'a ba su dai yi ĩmãni ba.
(34) Sai su zõ da wani lãbãri mai misãlinsa idan sun kasance sũmãsu gaskiya ne.
(35) Shin, an halitta su ne bã daga kõme ba, kõ kuwa sũ ne mãsu yin halitta?
(36) Shin, sun halitta sammai da ƙasa ne? Ã'a ba su dai yi ĩmãnin yaƙĩni ba.
(37) Shin, taskõkin Ubangijinka, sunã a wurinsu ne? Kõ kuwa sũ ne mãsu rinjãya?
(38) Shin, sunã da wani tsãni ne wanda suke (hawa sunã) saurãron (lãbãrin samã) a cikinsa? Sai mai saurarõnsu ya zo da wani dalĩli bayyananne.
(39) Shin, Yanã da 'ya'ya mãtã ne kuma kũ, kunã da ɗiya maza ne?
(40) Shin, kanã tambayar su wata ijãra ne, sabõda haka suka zama mãsu jin nauyin biyan tãrar?
(41) Shin, a wurinsu akwai ilmin gaibi, sabõda haka sunã rubũtãwa?
(42) Shin, sunã nufin wani kaidi ne? To, waɗanda suka kãfirta sũ ne waɗanda ake yi wa kaidi.
(43) Shin, sunã da wani abin bautãwa ne wanda bã Allah ba? Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke yi na shirki!
(44) Kuma idan sun ga wani ɓaɓɓake daga samã yãnã fãɗuwa, sai su ce wani girgije ne, mai hauhawar jũna.
(45) To, ka bar su, sai sun haɗu da yinin nan da za a sũmar da su a cikinsa.
(46) Rãnar da kaidinsu bã ya wadãtar masu da kõme, kuma bã a taimakon su.
(47) Kuma lalle, waɗannan da suka yi zãluncin, sunã da azãba (a nan dũniya) banda waccan, kuma mafi yawansu ba su sani ba.
(48) Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnunMu, kuma ka tsarkake Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).
(49) Kuma daga dare, sai ka tsarkake Shi (da tasbĩhin) dalõkacin jũyãwar taurãri.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022