الأعراف   سورة  : Al-A'raaf


سورة Sura   الأعراف   Al-A'raaf
حَقِيقٌ عَلَىٰ أَن لَّا أَقُولَ عَلَى اللَّهِ إِلَّا الْحَقَّ ۚ قَدْ جِئْتُكُم بِبَيِّنَةٍ مِّن رَّبِّكُمْ فَأَرْسِلْ مَعِيَ بَنِي إِسْرَائِيلَ (105) قَالَ إِن كُنتَ جِئْتَ بِآيَةٍ فَأْتِ بِهَا إِن كُنتَ مِنَ الصَّادِقِينَ (106) فَأَلْقَىٰ عَصَاهُ فَإِذَا هِيَ ثُعْبَانٌ مُّبِينٌ (107) وَنَزَعَ يَدَهُ فَإِذَا هِيَ بَيْضَاءُ لِلنَّاظِرِينَ (108) قَالَ الْمَلَأُ مِن قَوْمِ فِرْعَوْنَ إِنَّ هَٰذَا لَسَاحِرٌ عَلِيمٌ (109) يُرِيدُ أَن يُخْرِجَكُم مِّنْ أَرْضِكُمْ ۖ فَمَاذَا تَأْمُرُونَ (110) قَالُوا أَرْجِهْ وَأَخَاهُ وَأَرْسِلْ فِي الْمَدَائِنِ حَاشِرِينَ (111) يَأْتُوكَ بِكُلِّ سَاحِرٍ عَلِيمٍ (112) وَجَاءَ السَّحَرَةُ فِرْعَوْنَ قَالُوا إِنَّ لَنَا لَأَجْرًا إِن كُنَّا نَحْنُ الْغَالِبِينَ (113) قَالَ نَعَمْ وَإِنَّكُمْ لَمِنَ الْمُقَرَّبِينَ (114) قَالُوا يَا مُوسَىٰ إِمَّا أَن تُلْقِيَ وَإِمَّا أَن نَّكُونَ نَحْنُ الْمُلْقِينَ (115) قَالَ أَلْقُوا ۖ فَلَمَّا أَلْقَوْا سَحَرُوا أَعْيُنَ النَّاسِ وَاسْتَرْهَبُوهُمْ وَجَاءُوا بِسِحْرٍ عَظِيمٍ (116) ۞ وَأَوْحَيْنَا إِلَىٰ مُوسَىٰ أَنْ أَلْقِ عَصَاكَ ۖ فَإِذَا هِيَ تَلْقَفُ مَا يَأْفِكُونَ (117) فَوَقَعَ الْحَقُّ وَبَطَلَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (118) فَغُلِبُوا هُنَالِكَ وَانقَلَبُوا صَاغِرِينَ (119) وَأُلْقِيَ السَّحَرَةُ سَاجِدِينَ (120)
الصفحة Page 164
(105) "Tabbatacce ne a kan kada in faɗi kõme ga Allah fãce gaskiya. Lalle ne, nã zo muku da hujja bayyananniya daga Ubangijinku; Sai ka saki Banĩ Isrã'ila tãreda ni."
(106) Ya ce: "Idan kã kasance kã zo da wata ãyã, to, ka kãwõ ta, idan kã kasance daga mãsu gaskiya."
(107) Sai ya jẽfa sandarsa, sai gã ta kumurci bayyananne!
(108) Kuma ya fizge hannunsa, sai ga shi fari ga mãsu dũbi!
(109) Mashãwarta daga mutãnen Fir'auna suka ce: "Lalle ne, wannan, haƙĩƙa, matsafi ne mai ilmi."
(110) " Yanã son ya fitar da ku daga ƙasarku: To, mẽne ne kuke shawartawa?"
(111) Suka ce: "Ka jinkirtar da shĩ, shĩ da ɗan'uwansa, kuma ka aika da mãsu gayyar mutãne a cikin garũruwa.
(112) "Su zõ maka da duka matsafi, mai ilmi."
(113) Kuma matsafa suka jẽ wa fir'aunã suka ce: "Lalle ne, shin, Munã da ijãra, idan mun kasance mũ ne marinjaya?"
(114) Ya ce: "Na, am kuma lalle ne kunã a cikin makusanta."
(115) Suka ce: "Ya Mũsã! Kõ dai ka jẽfa, kõ kuwa mu kasance, mũ ne, mãsu jẽfãwa?"
(116) Ya ce: "Ku jẽfa." To a 1õkacin da suka jẽfa, suka sihirce idãnun mutãne kuma suka tsõratar da su; Kuma suka jẽ da tsafi mai girma."
(117) Kuma Muka yi wahayi zuwa ga Mũsã cẽwa: "Ka jẽfa sandarka." Sai gã ta tanã lãƙumar abin da suke ƙarya da shi!
(118) Gaskiya ta auku, kuma abin da suke aikatãwa ya ɓãci.
(119) Sai aka rinjãye su a can, kuma suka jũya sunã ƙasƙantattu.
(120) Kuma aka jẽfar da matsafan, sunã mãsu sujada.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022