الأعراف   سورة  : Al-A'raaf


سورة Sura   الأعراف   Al-A'raaf
قَالَ يَا مُوسَىٰ إِنِّي اصْطَفَيْتُكَ عَلَى النَّاسِ بِرِسَالَاتِي وَبِكَلَامِي فَخُذْ مَا آتَيْتُكَ وَكُن مِّنَ الشَّاكِرِينَ (144) وَكَتَبْنَا لَهُ فِي الْأَلْوَاحِ مِن كُلِّ شَيْءٍ مَّوْعِظَةً وَتَفْصِيلًا لِّكُلِّ شَيْءٍ فَخُذْهَا بِقُوَّةٍ وَأْمُرْ قَوْمَكَ يَأْخُذُوا بِأَحْسَنِهَا ۚ سَأُرِيكُمْ دَارَ الْفَاسِقِينَ (145) سَأَصْرِفُ عَنْ آيَاتِيَ الَّذِينَ يَتَكَبَّرُونَ فِي الْأَرْضِ بِغَيْرِ الْحَقِّ وَإِن يَرَوْا كُلَّ آيَةٍ لَّا يُؤْمِنُوا بِهَا وَإِن يَرَوْا سَبِيلَ الرُّشْدِ لَا يَتَّخِذُوهُ سَبِيلًا وَإِن يَرَوْا سَبِيلَ الْغَيِّ يَتَّخِذُوهُ سَبِيلًا ۚ ذَٰلِكَ بِأَنَّهُمْ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَكَانُوا عَنْهَا غَافِلِينَ (146) وَالَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا وَلِقَاءِ الْآخِرَةِ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ ۚ هَلْ يُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (147) وَاتَّخَذَ قَوْمُ مُوسَىٰ مِن بَعْدِهِ مِنْ حُلِيِّهِمْ عِجْلًا جَسَدًا لَّهُ خُوَارٌ ۚ أَلَمْ يَرَوْا أَنَّهُ لَا يُكَلِّمُهُمْ وَلَا يَهْدِيهِمْ سَبِيلًا ۘ اتَّخَذُوهُ وَكَانُوا ظَالِمِينَ (148) وَلَمَّا سُقِطَ فِي أَيْدِيهِمْ وَرَأَوْا أَنَّهُمْ قَدْ ضَلُّوا قَالُوا لَئِن لَّمْ يَرْحَمْنَا رَبُّنَا وَيَغْفِرْ لَنَا لَنَكُونَنَّ مِنَ الْخَاسِرِينَ (149)
الصفحة Page 168
(144) Ya ce: "Ya Mũsã! Lalle ne Nĩ, Nã zãɓe ka bisa ga mutãne da manzanciNa, kuma da maganãTa. Sabõda haka ka riƙi abin da Nã bã ka, kuma ka kasance daga mãsu gõdiya."
(145) Kuma Muka rubũta masa a cikin alluna daga kõwane abu, wa'azi da rarrabẽwa ga dukan kõwane abu: "Sai ka riƙe su da ƙarfi, kuma ka umurci mutãnenka, su yi riƙo ga abin da yake mafi kyawunsu; zã Ni nũna muku gidan fãsiƙai."
(146) Zã Ni karkatar da waɗanda suke yin girman kai a cikin ƙasa, bã da wani hakki ba, daga ãyõyiNa. Kuma idan sun ga dukan ãyã, bã zã su yi ĩmãni da ita ba, kuma idan sun ga hanyar shiriya, bã zã su riƙe ta hanya ba, kuma idan sun ga hanyar ɓata, sai su riƙe ta hanya. Wancan ne, dõmin lalle ne su, sun ƙaryata da ãyõyinMu, kuma sun kasance, daga barinsu gãfilai.
(147) Kuma waɗanda suka ƙaryata game da ãyõyinMu da gamuwa da Lãhira, ayyukansu sun ɓãci. Shin, ana saka musu, fãce da abin da suka kasance suna aikatãwa?
(148) Kuma mutãnen Mũsã suka riƙi maraƙi, jikin mutãne, yanã rũri, daga bãyan tafiyarsa, daga kãyan ƙawarsu. Shin, ba su ganĩ ba, cẽwa lalle ne shi, bã ya yi musu magana, kuma bã ya shiryar da su ga hanya, sun riƙa shi, kuma sun kasance mãsu zãlunci.
(149) Kuma a lõkacin da suka yi nadãma, kuma suka ga cẽwalalle ne sũ haƙĩƙa sun ɓace, suka ce: "Haƙĩƙa, idan UbangijinMu bai yi mana rahama ba, kuma Ya gãfarta mana, lalle ne munã kasancẽwa daga mãsu hasãra."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022