البقرة   سورة  : Al-Baqara


سورة Sura   البقرة   Al-Baqara
سَلْ بَنِي إِسْرَائِيلَ كَمْ آتَيْنَاهُم مِّنْ آيَةٍ بَيِّنَةٍ ۗ وَمَن يُبَدِّلْ نِعْمَةَ اللَّهِ مِن بَعْدِ مَا جَاءَتْهُ فَإِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ (211) زُيِّنَ لِلَّذِينَ كَفَرُوا الْحَيَاةُ الدُّنْيَا وَيَسْخَرُونَ مِنَ الَّذِينَ آمَنُوا ۘ وَالَّذِينَ اتَّقَوْا فَوْقَهُمْ يَوْمَ الْقِيَامَةِ ۗ وَاللَّهُ يَرْزُقُ مَن يَشَاءُ بِغَيْرِ حِسَابٍ (212) كَانَ النَّاسُ أُمَّةً وَاحِدَةً فَبَعَثَ اللَّهُ النَّبِيِّينَ مُبَشِّرِينَ وَمُنذِرِينَ وَأَنزَلَ مَعَهُمُ الْكِتَابَ بِالْحَقِّ لِيَحْكُمَ بَيْنَ النَّاسِ فِيمَا اخْتَلَفُوا فِيهِ ۚ وَمَا اخْتَلَفَ فِيهِ إِلَّا الَّذِينَ أُوتُوهُ مِن بَعْدِ مَا جَاءَتْهُمُ الْبَيِّنَاتُ بَغْيًا بَيْنَهُمْ ۖ فَهَدَى اللَّهُ الَّذِينَ آمَنُوا لِمَا اخْتَلَفُوا فِيهِ مِنَ الْحَقِّ بِإِذْنِهِ ۗ وَاللَّهُ يَهْدِي مَن يَشَاءُ إِلَىٰ صِرَاطٍ مُّسْتَقِيمٍ (213) أَمْ حَسِبْتُمْ أَن تَدْخُلُوا الْجَنَّةَ وَلَمَّا يَأْتِكُم مَّثَلُ الَّذِينَ خَلَوْا مِن قَبْلِكُم ۖ مَّسَّتْهُمُ الْبَأْسَاءُ وَالضَّرَّاءُ وَزُلْزِلُوا حَتَّىٰ يَقُولَ الرَّسُولُ وَالَّذِينَ آمَنُوا مَعَهُ مَتَىٰ نَصْرُ اللَّهِ ۗ أَلَا إِنَّ نَصْرَ اللَّهِ قَرِيبٌ (214) يَسْأَلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَ ۖ قُلْ مَا أَنفَقْتُم مِّنْ خَيْرٍ فَلِلْوَالِدَيْنِ وَالْأَقْرَبِينَ وَالْيَتَامَىٰ وَالْمَسَاكِينِ وَابْنِ السَّبِيلِ ۗ وَمَا تَفْعَلُوا مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ اللَّهَ بِهِ عَلِيمٌ (215)
الصفحة Page 33
(211) Ka tambayi Banĩ Isrã'ila, da yawa Muka bã su daga ãyõyi bayyanannu. Kuma wanda ya musanya ni'imar Allah daga bãyan tã je masa, to, lalle ne Allah Mai tsananin uƙũba ne.
(212) An ƙawata rãyuwar dũniya ga waɗanda suka kãfirta, kuma suna izgili daga waɗanda suka yi ĩmãni, alhãli waɗanda suka yi taƙawa suna bisa gare su, a Rãnar ¡iyãma. Kuma Allah Yana azurta wanda Yake so, bã da lissãfi ba.
(213) Mutãne sun kasance al'umma guda. Sai Allah Ya aiki annabãwa suna mãsu bãyar da bishãra kuma mãsu gargaɗi; kuma Ya saukar da Littãfi da gaskiya tãre da su dõmin (Littãfin) ya yi hukunci a tsakãnin mutãnen a cikin abin da suka sãɓã wa jũna a cikinsa. kuma bãbu wanda ya sãɓã, a cikinsa, fãce waɗanda aka bai wa shi daga bãyan hujjõji bayyanannu sun je musu dõmin zãlunci a tsakãninsu. Sai Allah Ya shiryar da waɗanda suka yi ĩmani ga abin da suka sãɓã a cikinsa daga gaskiya da izninSa. Kuma Allah Yana shiryar da wanda Yake so, zuwa ga hanya madaidaiciya.
(214) Ko kuna zaton ku shiga Aljanna kuma tun misãlin waɗanda suka shige daga gabãninku bai zo muku ba? Wahalõli da cũta sun shãfe su, kuma aka tsõratar da su har manzonsu da waɗanda suka yi ĩmãni tãre da shi su ce: "Yaushe taimakon Allah zai zo?" To! Lalle ne, taimakon Allah yana kusa!
(215) Suna tambayar ka mẽne nezã su ciyar. Ka ce: Abin da kuka ciyar daga alhẽri sai ga mahaifa da mafi kusantar dangantaka da marãyu da matalauta da ɗan hanya. Kuma abin da kuka aikata daga alhẽri, to, lalle ne, Allah gare shi Masani ne.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022