البقرة   سورة  : Al-Baqara


سورة Sura   البقرة   Al-Baqara
وَمَا أَنفَقْتُم مِّن نَّفَقَةٍ أَوْ نَذَرْتُم مِّن نَّذْرٍ فَإِنَّ اللَّهَ يَعْلَمُهُ ۗ وَمَا لِلظَّالِمِينَ مِنْ أَنصَارٍ (270) إِن تُبْدُوا الصَّدَقَاتِ فَنِعِمَّا هِيَ ۖ وَإِن تُخْفُوهَا وَتُؤْتُوهَا الْفُقَرَاءَ فَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۚ وَيُكَفِّرُ عَنكُم مِّن سَيِّئَاتِكُمْ ۗ وَاللَّهُ بِمَا تَعْمَلُونَ خَبِيرٌ (271) ۞ لَّيْسَ عَلَيْكَ هُدَاهُمْ وَلَٰكِنَّ اللَّهَ يَهْدِي مَن يَشَاءُ ۗ وَمَا تُنفِقُوا مِنْ خَيْرٍ فَلِأَنفُسِكُمْ ۚ وَمَا تُنفِقُونَ إِلَّا ابْتِغَاءَ وَجْهِ اللَّهِ ۚ وَمَا تُنفِقُوا مِنْ خَيْرٍ يُوَفَّ إِلَيْكُمْ وَأَنتُمْ لَا تُظْلَمُونَ (272) لِلْفُقَرَاءِ الَّذِينَ أُحْصِرُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ لَا يَسْتَطِيعُونَ ضَرْبًا فِي الْأَرْضِ يَحْسَبُهُمُ الْجَاهِلُ أَغْنِيَاءَ مِنَ التَّعَفُّفِ تَعْرِفُهُم بِسِيمَاهُمْ لَا يَسْأَلُونَ النَّاسَ إِلْحَافًا ۗ وَمَا تُنفِقُوا مِنْ خَيْرٍ فَإِنَّ اللَّهَ بِهِ عَلِيمٌ (273) الَّذِينَ يُنفِقُونَ أَمْوَالَهُم بِاللَّيْلِ وَالنَّهَارِ سِرًّا وَعَلَانِيَةً فَلَهُمْ أَجْرُهُمْ عِندَ رَبِّهِمْ وَلَا خَوْفٌ عَلَيْهِمْ وَلَا هُمْ يَحْزَنُونَ (274)
الصفحة Page 46
(270) Kuma abin da kuka ciyar daga ciyarwa, kõ kuka cika alwãshi daga wani bãkance, to, lalle ne, Allah Yana sanin sa. Kuma azzãlumai bã su da wasu mataimaka.
(271) Idan kun nũna sadakõki to, yana da kyau ƙwarai kuma idan kuka ɓõye su kuma kuka je da su ga matalauta, to shi ne mafi alhẽri a gareku, kuma Yana kankarẽwa, daga barinku, daga miyãgun ayyukanku. Kuma Allah ga abin da kuke aikatawa Masani ne.
(272) Shiryar da su bã ya a kanka, kuma amma Allah Shi ne Yake shiryar da wanda Yake so, kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, dõmin kanku ne, kuma bã ku ciyarwa, fãce dõmin nẽman yardar Allah, kuma abin da kuke ciyarwa daga alhẽri zã a cika lãdarsa zuwa gare ku, alhãli kuwa kũ bã a zãluntarku.
(273) (Ciyarwar a yĩ ta) ga matalautan nan waɗanda aka tsare a cikin hanyar Allah, ba su iya tafiyar fatauci a cikin ƙasa, jãhilin hãlinsu yana zaton su wadãtattu sabõda kãmun kai kana sanin su da alãmarsu, ba su rõƙon mutãne da nãcẽwa. Kuma abin da kuka ciyar daga alhẽri, to, lalle Allah gare shi Masani ne.
(274) Waɗanda suke ciyar da dukiyõyinsu, a dare da yini, ɓõye da bayyane, to suna da sakamakonsu a wurin Ubangijinsu. Kuma bãbu tsõro a kansu, kuma ba su zama suna baƙin ciki ba.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022