البقرة   سورة  : Al-Baqara


سورة Sura   البقرة   Al-Baqara
كُتِبَ عَلَيْكُمُ الْقِتَالُ وَهُوَ كُرْهٌ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰ أَن تَكْرَهُوا شَيْئًا وَهُوَ خَيْرٌ لَّكُمْ ۖ وَعَسَىٰ أَن تُحِبُّوا شَيْئًا وَهُوَ شَرٌّ لَّكُمْ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ وَأَنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ (216) يَسْأَلُونَكَ عَنِ الشَّهْرِ الْحَرَامِ قِتَالٍ فِيهِ ۖ قُلْ قِتَالٌ فِيهِ كَبِيرٌ ۖ وَصَدٌّ عَن سَبِيلِ اللَّهِ وَكُفْرٌ بِهِ وَالْمَسْجِدِ الْحَرَامِ وَإِخْرَاجُ أَهْلِهِ مِنْهُ أَكْبَرُ عِندَ اللَّهِ ۚ وَالْفِتْنَةُ أَكْبَرُ مِنَ الْقَتْلِ ۗ وَلَا يَزَالُونَ يُقَاتِلُونَكُمْ حَتَّىٰ يَرُدُّوكُمْ عَن دِينِكُمْ إِنِ اسْتَطَاعُوا ۚ وَمَن يَرْتَدِدْ مِنكُمْ عَن دِينِهِ فَيَمُتْ وَهُوَ كَافِرٌ فَأُولَٰئِكَ حَبِطَتْ أَعْمَالُهُمْ فِي الدُّنْيَا وَالْآخِرَةِ ۖ وَأُولَٰئِكَ أَصْحَابُ النَّارِ ۖ هُمْ فِيهَا خَالِدُونَ (217) إِنَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَالَّذِينَ هَاجَرُوا وَجَاهَدُوا فِي سَبِيلِ اللَّهِ أُولَٰئِكَ يَرْجُونَ رَحْمَتَ اللَّهِ ۚ وَاللَّهُ غَفُورٌ رَّحِيمٌ (218) ۞ يَسْأَلُونَكَ عَنِ الْخَمْرِ وَالْمَيْسِرِ ۖ قُلْ فِيهِمَا إِثْمٌ كَبِيرٌ وَمَنَافِعُ لِلنَّاسِ وَإِثْمُهُمَا أَكْبَرُ مِن نَّفْعِهِمَا ۗ وَيَسْأَلُونَكَ مَاذَا يُنفِقُونَ قُلِ الْعَفْوَ ۗ كَذَٰلِكَ يُبَيِّنُ اللَّهُ لَكُمُ الْآيَاتِ لَعَلَّكُمْ تَتَفَكَّرُونَ (219)
الصفحة Page 34
(216) An wajabta yãƙi a kanku, alhãli kuwa shi abin ƙi ne a gare ku, akwai fãtar cẽwa ku ƙi wani abu, alhãli shi ne mafi alhẽri a gare ku, kumaakwai fãtar cẽwa kuna son wani abu alhãli kuwa shi ne mafi sharri a gare ku. Kuma Allah ne Yake sani, kuma kũ ba ku sani ba.
(217) Suna tambayar ka game da Watan Alfarma: yin yãki a cikinsa. Ka ce: "Yin yãƙi a cikinsa babban zunubi ne, kuma hani daga hanyar Allah, da kuma kãfirci da Shi, da kuma da Masallaci Tsararre, da Kuma fitar da mutãnensa daga gare shi, shi ne mafi girman zunubi a wurin Allah." Kuma fitina ita ce mafi girma daga kisa. Kuma bã su gushẽwa suna yãƙinku har su mayar da ku daga barin addininku idan za su iya. Kuma wanda ya yi ridda daga gare ku ga barin addininsa har ya mutu alhãli kuwa yana kãfiri, to, waɗannan ayyukansu sun ɓãci a cikin dũniya da Lãhira. Kuma waɗannan abõkan Wuta ne, sũ a cikinta madawwama ne.
(218) Lalle ne waɗanda suka yi ĩmãni, da waɗanda suka yi hijira kuma suka yi jihãdi a cikin hanyar Allah waɗannan suna fãtar (sãmun) rahamar Allah kuma Allah Mai gãfara ne, Mai jin ƙai.
(219) Suna tambayar ka game da giya da cãcã. Ka ce: "A cikinsu akwai zunubi mai girma da wasu amfãnõni ga mutãne, kuma zunubinsu ne mafi girma daga amfaninsu." Kuma suna tambayar ka mẽne ne zã su ciyar; ka ce: "Abin da ya rage." Kamar wancan ne Allah Yake bayyanawar ãyõyi a gare ku; tsammãninku, kuna tunãni.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022