الأنبياء   سورة  : Al-Anbiyaa


سورة Sura   الأنبياء   Al-Anbiyaa
الأنبياء Al-Anbiyaa
اقْتَرَبَ لِلنَّاسِ حِسَابُهُمْ وَهُمْ فِي غَفْلَةٍ مُّعْرِضُونَ (1) مَا يَأْتِيهِم مِّن ذِكْرٍ مِّن رَّبِّهِم مُّحْدَثٍ إِلَّا اسْتَمَعُوهُ وَهُمْ يَلْعَبُونَ (2) لَاهِيَةً قُلُوبُهُمْ ۗ وَأَسَرُّوا النَّجْوَى الَّذِينَ ظَلَمُوا هَلْ هَٰذَا إِلَّا بَشَرٌ مِّثْلُكُمْ ۖ أَفَتَأْتُونَ السِّحْرَ وَأَنتُمْ تُبْصِرُونَ (3) قَالَ رَبِّي يَعْلَمُ الْقَوْلَ فِي السَّمَاءِ وَالْأَرْضِ ۖ وَهُوَ السَّمِيعُ الْعَلِيمُ (4) بَلْ قَالُوا أَضْغَاثُ أَحْلَامٍ بَلِ افْتَرَاهُ بَلْ هُوَ شَاعِرٌ فَلْيَأْتِنَا بِآيَةٍ كَمَا أُرْسِلَ الْأَوَّلُونَ (5) مَا آمَنَتْ قَبْلَهُم مِّن قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا ۖ أَفَهُمْ يُؤْمِنُونَ (6) وَمَا أَرْسَلْنَا قَبْلَكَ إِلَّا رِجَالًا نُّوحِي إِلَيْهِمْ ۖ فَاسْأَلُوا أَهْلَ الذِّكْرِ إِن كُنتُمْ لَا تَعْلَمُونَ (7) وَمَا جَعَلْنَاهُمْ جَسَدًا لَّا يَأْكُلُونَ الطَّعَامَ وَمَا كَانُوا خَالِدِينَ (8) ثُمَّ صَدَقْنَاهُمُ الْوَعْدَ فَأَنجَيْنَاهُمْ وَمَن نَّشَاءُ وَأَهْلَكْنَا الْمُسْرِفِينَ (9) لَقَدْ أَنزَلْنَا إِلَيْكُمْ كِتَابًا فِيهِ ذِكْرُكُمْ ۖ أَفَلَا تَعْقِلُونَ (10)
الصفحة Page 322
الأنبياء Al-Anbiyaa
(1) Hisãbin mutãne ya kusanta gare su, ahãli kuwa sunã a cikin gafala, sunã mãsu bijirẽwa.
(2) Wani ambatõ daga Ubangijinsu sãbo, bã ya zuwa gare su fãce sun saurãre shi, alhãli kuwa sunã mãsu yin wãsa.
(3) Sanã mãsu shagaltacin zukãtansu, kuma su asirta gãnãwa: Waɗanda suka yi zãlunce (sunã cẽwa) "Wannan bã Kõwa ba ne fãce mutum misãlinku. Shin, to, kunã jẽ wa sihiri, ahãli kuwa kũ, kunã fahimta?"
(4) Ya ce: "Ubangijina Yanã sanin magana a cikin sama da ƙasa kuma Shi ne Mai ji, Masani."
(5) Ã'a, suka ce: "Yãye-yãyen mafarki ne. Ã'a, yã ƙirƙira shi ne. Ã'a, shi mawãƙi ne. Sai ya zo mana da wata ãyã kamar yadda aka aiko manzanni na farko."
(6) Wata alƙarya da Muka halaka ta a gabãninsu, ba ta yi ĩmãni ba. Shin, to, sũ, sunã yin ĩmãni?
(7) Kuma ba Mu aika ba a gabãninka fãce mazãje, Munã yin wahayi zuwa gare su. Ku tambayi ma'abũta ambato idan kun kasance ba ku sani ba.
(8) Kuma ba Mu sanya su jiki, bã su cin abin ci ba, kuma ba su kasance madawwama ba.
(9) Sa'an nan kuma Muka gaskata musu alkawari; sai Muka tsẽrar da su da wanda Muke so, kuma Muka halakar da mãsu yawaitãwa.
(10) Lalle haƙĩƙa Mun saukar da wani littãfi zuwa gare ku, a cikinsa akwai ambatonku. Shin, to, bã ku hankalta?
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022