الأنبياء   سورة  : Al-Anbiyaa


سورة Sura   الأنبياء   Al-Anbiyaa
وَالَّتِي أَحْصَنَتْ فَرْجَهَا فَنَفَخْنَا فِيهَا مِن رُّوحِنَا وَجَعَلْنَاهَا وَابْنَهَا آيَةً لِّلْعَالَمِينَ (91) إِنَّ هَٰذِهِ أُمَّتُكُمْ أُمَّةً وَاحِدَةً وَأَنَا رَبُّكُمْ فَاعْبُدُونِ (92) وَتَقَطَّعُوا أَمْرَهُم بَيْنَهُمْ ۖ كُلٌّ إِلَيْنَا رَاجِعُونَ (93) فَمَن يَعْمَلْ مِنَ الصَّالِحَاتِ وَهُوَ مُؤْمِنٌ فَلَا كُفْرَانَ لِسَعْيِهِ وَإِنَّا لَهُ كَاتِبُونَ (94) وَحَرَامٌ عَلَىٰ قَرْيَةٍ أَهْلَكْنَاهَا أَنَّهُمْ لَا يَرْجِعُونَ (95) حَتَّىٰ إِذَا فُتِحَتْ يَأْجُوجُ وَمَأْجُوجُ وَهُم مِّن كُلِّ حَدَبٍ يَنسِلُونَ (96) وَاقْتَرَبَ الْوَعْدُ الْحَقُّ فَإِذَا هِيَ شَاخِصَةٌ أَبْصَارُ الَّذِينَ كَفَرُوا يَا وَيْلَنَا قَدْ كُنَّا فِي غَفْلَةٍ مِّنْ هَٰذَا بَلْ كُنَّا ظَالِمِينَ (97) إِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ مِن دُونِ اللَّهِ حَصَبُ جَهَنَّمَ أَنتُمْ لَهَا وَارِدُونَ (98) لَوْ كَانَ هَٰؤُلَاءِ آلِهَةً مَّا وَرَدُوهَا ۖ وَكُلٌّ فِيهَا خَالِدُونَ (99) لَهُمْ فِيهَا زَفِيرٌ وَهُمْ فِيهَا لَا يَسْمَعُونَ (100) إِنَّ الَّذِينَ سَبَقَتْ لَهُم مِّنَّا الْحُسْنَىٰ أُولَٰئِكَ عَنْهَا مُبْعَدُونَ (101)
الصفحة Page 330
(91) Kuma da wadda ta tsare farJinta daga alfãsha. Sai Muka hũra a cikinta daga rũhinMu. Kuma Muka sanya ta ita da ɗanta wata ãyã ga dũniya.
(92) Lalle ne wannan ita ce al'ummarku ta zama al'umma guda, kuma Nĩ ne Ubangijinku. Sai ku bauta Mini.
(93) Kuma suka kakkãtse al'amarinsu a tsakaninsu. Dukan Kõwanensu mãsu Kõmõwa zuwa gare Ni
(94) Dõmin wanda ya aikata daga ayyukan kwarai alhãli kuwa yanã mai ĩmãni, to, bãbu musu ga aikinsa, kuma Mu Mãsu rubũtãwa gare shi ne.
(95) Kuma hananne ne a kan wata alƙarya da Muka halakar cẽwa lalle sũ, bã su kõmõwa.
(96) Har sa'ad da aka bũde Yãjũju da Mãjũju alhãli kuwa sunã gaggãwa daga kõwane tudun ƙasa.
(97) Kuma wa'adin nan tabbatacce ya kusanto, sai gã ta idãnun waɗanda suka kãfirta sunã bayyanannu, (sunã cẽwa), "Yã kaitonmu! Haƙĩƙa mun kasance a cikin gafala daga wannan! Ã'a, mun kasance dai mãsu zãlunci!"
(98) (A ce musu) "Lalle ne, kũ da abin da kuke bautãwa, baicin Allah makãmashin Jahannama ne. Kũ mãsu tusgãwa gare ta ne."
(99) Dã waɗannan (abũbuwanbautãwar) sun kasance abũbuwan bautãwar gaskiya ne, dã ba su tusga mata ba, alhãli kuwa dukansu madawwama a cikinta ne.
(100) Sunã da wata hargõwa a cikinta, alhãli kuwa sũ, a cikinta, bã su saurãren kõme.
(101) Lalle ne waɗanda kalmar yabo tã gabãta a garẽ su daga garẽ Mu, waɗannan waɗanda ake nĩsantarwa daga barinta ne.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022