الأنبياء   سورة  : Al-Anbiyaa


سورة Sura   الأنبياء   Al-Anbiyaa
وَجَعَلْنَاهُمْ أَئِمَّةً يَهْدُونَ بِأَمْرِنَا وَأَوْحَيْنَا إِلَيْهِمْ فِعْلَ الْخَيْرَاتِ وَإِقَامَ الصَّلَاةِ وَإِيتَاءَ الزَّكَاةِ ۖ وَكَانُوا لَنَا عَابِدِينَ (73) وَلُوطًا آتَيْنَاهُ حُكْمًا وَعِلْمًا وَنَجَّيْنَاهُ مِنَ الْقَرْيَةِ الَّتِي كَانَت تَّعْمَلُ الْخَبَائِثَ ۗ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمَ سَوْءٍ فَاسِقِينَ (74) وَأَدْخَلْنَاهُ فِي رَحْمَتِنَا ۖ إِنَّهُ مِنَ الصَّالِحِينَ (75) وَنُوحًا إِذْ نَادَىٰ مِن قَبْلُ فَاسْتَجَبْنَا لَهُ فَنَجَّيْنَاهُ وَأَهْلَهُ مِنَ الْكَرْبِ الْعَظِيمِ (76) وَنَصَرْنَاهُ مِنَ الْقَوْمِ الَّذِينَ كَذَّبُوا بِآيَاتِنَا ۚ إِنَّهُمْ كَانُوا قَوْمَ سَوْءٍ فَأَغْرَقْنَاهُمْ أَجْمَعِينَ (77) وَدَاوُودَ وَسُلَيْمَانَ إِذْ يَحْكُمَانِ فِي الْحَرْثِ إِذْ نَفَشَتْ فِيهِ غَنَمُ الْقَوْمِ وَكُنَّا لِحُكْمِهِمْ شَاهِدِينَ (78) فَفَهَّمْنَاهَا سُلَيْمَانَ ۚ وَكُلًّا آتَيْنَا حُكْمًا وَعِلْمًا ۚ وَسَخَّرْنَا مَعَ دَاوُودَ الْجِبَالَ يُسَبِّحْنَ وَالطَّيْرَ ۚ وَكُنَّا فَاعِلِينَ (79) وَعَلَّمْنَاهُ صَنْعَةَ لَبُوسٍ لَّكُمْ لِتُحْصِنَكُم مِّن بَأْسِكُمْ ۖ فَهَلْ أَنتُمْ شَاكِرُونَ (80) وَلِسُلَيْمَانَ الرِّيحَ عَاصِفَةً تَجْرِي بِأَمْرِهِ إِلَى الْأَرْضِ الَّتِي بَارَكْنَا فِيهَا ۚ وَكُنَّا بِكُلِّ شَيْءٍ عَالِمِينَ (81)
الصفحة Page 328
(73) Kuma Muka sanya su shugabanni, sunã shiryarwa da umurninMu. Kuma Muka yi wahayi zuwa gare su da ayyukan alhẽri da tsayar da salla da bãyar da zakka. Kuma sun kasance mãsu bauta gare Mu.
(74) Kuma Lũɗu Mun bã shi hukunci da ilmi. Kuma Mun tsĩrar da shi daga alƙaryar nan wadda ke aikata mũnãnan ayyuka. Lallesũ, sun kasance mutãnen mũgun aiki, fãsiƙai.
(75) Kuma Muka shigar da shi a cikin rahamarMu. Lalle ne shĩ, yanã daga sãlihai.
(76) Kuma Nũhu, a sa'ad da ya yi kira a gabãni, sai Muka karɓa masa, sa'an nan Muka tsirar da shi da mutãnensa daga baƙin ciki mai girma.
(77) Kuma Muka taimake shi daga mutãnen nan waɗanda suka ƙaryata da ãyõyinMu. Lalle ne sũ, sun kasance mutãnen mugun aiki. Sai Muka nutsar da su gabã ɗaya.
(78) Kuma Dãwũda da Sulaimãn sa'ad da suke yin hukunci a cikin sha'anin shũka a lõkacin da tumãkin mutãne suka yi kiĩwon dare a cikinsa. Kuma Mun kasance Mãsu halarta ga hukuncinsu.
(79) Sai Muka fahimtar da ita (mats'alar) ga Sulaiman. Kuma dukansu Mun bã su hukunci da ilmi kuma Muka hõre duwatsu tãre da Dãwũda, sunã tasbĩhi, da tsuntsãye. Kuma Mun kasance Mãsu aikatãwa.
(80) Kuma Muka sanar da shi sana'ar wata tufa sabõda ku dõmin ya tsare ku daga makãminku. To, shin, ku mãsu gõdẽwa ne?
(81) Kuma (Muka hõre) wa Sulaimãn iska mai tsananin bugãwa, tanã gudãna da umuruinsa zuwa ga ƙasar nan wadda Muka sanya albarka a cikinta. Kuma Mun kasance Masana ga dukkan Kõme.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022