المطففين   سورة  : Al-Mutaffifin


سورة Sura   المطففين   Al-Mutaffifin
عَلَى الْأَرَائِكِ يَنظُرُونَ (35) هَلْ ثُوِّبَ الْكُفَّارُ مَا كَانُوا يَفْعَلُونَ (36)
الإنشقاق Al-Inshiqaaq
إِذَا السَّمَاءُ انشَقَّتْ (1) وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ (2) وَإِذَا الْأَرْضُ مُدَّتْ (3) وَأَلْقَتْ مَا فِيهَا وَتَخَلَّتْ (4) وَأَذِنَتْ لِرَبِّهَا وَحُقَّتْ (5) يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ إِنَّكَ كَادِحٌ إِلَىٰ رَبِّكَ كَدْحًا فَمُلَاقِيهِ (6) فَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ بِيَمِينِهِ (7) فَسَوْفَ يُحَاسَبُ حِسَابًا يَسِيرًا (8) وَيَنقَلِبُ إِلَىٰ أَهْلِهِ مَسْرُورًا (9) وَأَمَّا مَنْ أُوتِيَ كِتَابَهُ وَرَاءَ ظَهْرِهِ (10) فَسَوْفَ يَدْعُو ثُبُورًا (11) وَيَصْلَىٰ سَعِيرًا (12) إِنَّهُ كَانَ فِي أَهْلِهِ مَسْرُورًا (13) إِنَّهُ ظَنَّ أَن لَّن يَحُورَ (14) بَلَىٰ إِنَّ رَبَّهُ كَانَ بِهِ بَصِيرًا (15) فَلَا أُقْسِمُ بِالشَّفَقِ (16) وَاللَّيْلِ وَمَا وَسَقَ (17) وَالْقَمَرِ إِذَا اتَّسَقَ (18) لَتَرْكَبُنَّ طَبَقًا عَن طَبَقٍ (19) فَمَا لَهُمْ لَا يُؤْمِنُونَ (20) وَإِذَا قُرِئَ عَلَيْهِمُ الْقُرْآنُ لَا يَسْجُدُونَ ۩ (21) بَلِ الَّذِينَ كَفَرُوا يُكَذِّبُونَ (22) وَاللَّهُ أَعْلَمُ بِمَا يُوعُونَ (23) فَبَشِّرْهُم بِعَذَابٍ أَلِيمٍ (24) إِلَّا الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ لَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍ (25)
الصفحة Page 589
(35) A kan karagu, suna ta kallo.
(36) Shin an sãka ma kãfirai abin da suka kasance suna aikatawa?
الإنشقاق Al-Inshiqaaq
(1) Idan sama ta kẽce,
(2) Ta saurari Ubangijinta, kuma aka wajabta mata yin saurãron,
(3) Kuma idan ƙasã aka mĩƙe ta,
(4) Kuma ta jẽfar da abin da yake a cikinta, tã wõfinta daga kõme.
(5) Kuma ta saurãri Ubangijinta, aka wajabta mata yin saurãren,
(6) Ya kai mutum! Lalle ne kai mai aikin wahal da kai ne zuwa ga Ubangijinka, wahala mai tsanani, To, kai mai haɗuwa da Shi ne.
(7) To, amma wanda aka bai wa littãfinsa da damansa.
(8) To, za a yi masa hisãbi, hisãbi mai sauƙi.
(9) Kuma ya jũya zuwa ga iyãlinsa (a cikin Aljanna), yanã mai raha.
(10) Kuma amma wanda aka bai wa littãfinsa, daga wajen bãyansa.
(11) To, zã shi dinga kiran halaka!
(12) Kuma ya shiga sa'ĩr.
(13) Lal1e ne shi, yã kasance (a dũniya) cikin iyãlinsa yanã mai raha.
(14) Lalle ne yã yi zaton bã zai kõmo ba.
(15) Na'am! Lalle ne, Ubangijinsa Ya kasance Mai gani gare shi.
(16) To, ba sai Nã rantse da shafaƙi ba.
(17) Da dare, da abin da ya ƙunsa.
(18) Da watã idan (haskensa) ya cika.
(19) Lalle ne kunã hawan wani hãli daga wani hãli.
(20) To, mẽ ya sãme su, ba su yin ĩmãni?
(21) Kuma idan an karanta Alkur'ãni a kansu, bã su yin tawãli'u?
(22) Ba haka ba! waɗanda suka kãfirta, sai ƙaryatãwa suke yi.
(23) Alhãli Allah Shĩ ne Mafi sani ga abin a suke tãrãwa.
(24) Saboda haka, ka yi musu bushãra da azãba mai raɗaɗi.
(25) Fãce waɗanda suka yi ĩmãni, suka aikata ayyukan ƙwarai, sunã da wani sakamako wanda bã ya yankẽwa.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022