المطففين   سورة  : Al-Mutaffifin


سورة Sura   المطففين   Al-Mutaffifin
الإنفطار Al-Infitaar
إِذَا السَّمَاءُ انفَطَرَتْ (1) وَإِذَا الْكَوَاكِبُ انتَثَرَتْ (2) وَإِذَا الْبِحَارُ فُجِّرَتْ (3) وَإِذَا الْقُبُورُ بُعْثِرَتْ (4) عَلِمَتْ نَفْسٌ مَّا قَدَّمَتْ وَأَخَّرَتْ (5) يَا أَيُّهَا الْإِنسَانُ مَا غَرَّكَ بِرَبِّكَ الْكَرِيمِ (6) الَّذِي خَلَقَكَ فَسَوَّاكَ فَعَدَلَكَ (7) فِي أَيِّ صُورَةٍ مَّا شَاءَ رَكَّبَكَ (8) كَلَّا بَلْ تُكَذِّبُونَ بِالدِّينِ (9) وَإِنَّ عَلَيْكُمْ لَحَافِظِينَ (10) كِرَامًا كَاتِبِينَ (11) يَعْلَمُونَ مَا تَفْعَلُونَ (12) إِنَّ الْأَبْرَارَ لَفِي نَعِيمٍ (13) وَإِنَّ الْفُجَّارَ لَفِي جَحِيمٍ (14) يَصْلَوْنَهَا يَوْمَ الدِّينِ (15) وَمَا هُمْ عَنْهَا بِغَائِبِينَ (16) وَمَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ (17) ثُمَّ مَا أَدْرَاكَ مَا يَوْمُ الدِّينِ (18) يَوْمَ لَا تَمْلِكُ نَفْسٌ لِّنَفْسٍ شَيْئًا ۖ وَالْأَمْرُ يَوْمَئِذٍ لِّلَّهِ (19)
المطففين Al-Mutaffifin
وَيْلٌ لِّلْمُطَفِّفِينَ (1) الَّذِينَ إِذَا اكْتَالُوا عَلَى النَّاسِ يَسْتَوْفُونَ (2) وَإِذَا كَالُوهُمْ أَو وَّزَنُوهُمْ يُخْسِرُونَ (3) أَلَا يَظُنُّ أُولَٰئِكَ أَنَّهُم مَّبْعُوثُونَ (4) لِيَوْمٍ عَظِيمٍ (5) يَوْمَ يَقُومُ النَّاسُ لِرَبِّ الْعَالَمِينَ (6)
الصفحة Page 587
الإنفطار Al-Infitaar
(1) Idan sama ta tsãge.
(2) Kuma idan taurãri suka wãtse.
(3) Kuma idan tẽkuna aka facce su.
(4) Kuma idan kaburbura aka tõne su.
(5) Rai yã san abin da ya gabatar, da abin da yã jinkirtar.
(6) Yã kai mutum! Mẽ ya rũɗe ka game da Ubangijinka, Mai karimci.
(7) Wanda Ya halitta ka sa'an nan ya daidaitã ka, Ya kuma tsakaitã ka.
(8) A cikin kõwace irin sũra Ya so Ya ginã ka a kanta.
(9) A'aha, bã haka ba, kuna ƙaryatãwa game da sakamako!
(10) Lalle ne, a kanku, haƙiƙa akwai matsara.
(11) Mãsu daraja, marubũta.
(12) Sunã sanin abin da kuke aikatãwa.
(13) Lalle ne, mãsu ɗã'ã ga Allah, dãhir, suna cikin ni'ima.
(14) Kuma lalle ne, fãjirai, dãhir, sunã cikin Jahĩm.
(15) Zã su shigẽ ta a rãnar sakamako.
(16) Bã zã su faku daga gare ta ba.
(17) Kuma mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rẽnar sakamako?
(18) Sa'an nan, mẽ ya sanar da kai abin da ake cẽ wa rãnar sakamako?
(19) Rãnã ce da wani rai ba ya iya mallakar kõme dõmin wani rai al'amari, a rãnar nan, ga Allah (ɗai) yake.
المطففين Al-Mutaffifin
(1) Bone ya tabbata ga mãsu naƙƙasãwa.
(2) Waɗanda suke idan suka auna daga mutãne suna cika mũdu.
(3) Kuma idan sun auna musu da zakka ko da sikẽli, suna ragẽwa
(4) Ashe! Waɗancan bã su tabbata cẽwa lalle sũ, ana tãyar da su ba?
(5) Domin yini mai girma.
(6) Yinin da mutãne ke tãshi zuwa ga Ubangijin halitta?
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022