التوبة   سورة  : At-Tawba


سورة Sura   التوبة   At-Tawba
التَّائِبُونَ الْعَابِدُونَ الْحَامِدُونَ السَّائِحُونَ الرَّاكِعُونَ السَّاجِدُونَ الْآمِرُونَ بِالْمَعْرُوفِ وَالنَّاهُونَ عَنِ الْمُنكَرِ وَالْحَافِظُونَ لِحُدُودِ اللَّهِ ۗ وَبَشِّرِ الْمُؤْمِنِينَ (112) مَا كَانَ لِلنَّبِيِّ وَالَّذِينَ آمَنُوا أَن يَسْتَغْفِرُوا لِلْمُشْرِكِينَ وَلَوْ كَانُوا أُولِي قُرْبَىٰ مِن بَعْدِ مَا تَبَيَّنَ لَهُمْ أَنَّهُمْ أَصْحَابُ الْجَحِيمِ (113) وَمَا كَانَ اسْتِغْفَارُ إِبْرَاهِيمَ لِأَبِيهِ إِلَّا عَن مَّوْعِدَةٍ وَعَدَهَا إِيَّاهُ فَلَمَّا تَبَيَّنَ لَهُ أَنَّهُ عَدُوٌّ لِّلَّهِ تَبَرَّأَ مِنْهُ ۚ إِنَّ إِبْرَاهِيمَ لَأَوَّاهٌ حَلِيمٌ (114) وَمَا كَانَ اللَّهُ لِيُضِلَّ قَوْمًا بَعْدَ إِذْ هَدَاهُمْ حَتَّىٰ يُبَيِّنَ لَهُم مَّا يَتَّقُونَ ۚ إِنَّ اللَّهَ بِكُلِّ شَيْءٍ عَلِيمٌ (115) إِنَّ اللَّهَ لَهُ مُلْكُ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضِ ۖ يُحْيِي وَيُمِيتُ ۚ وَمَا لَكُم مِّن دُونِ اللَّهِ مِن وَلِيٍّ وَلَا نَصِيرٍ (116) لَّقَد تَّابَ اللَّهُ عَلَى النَّبِيِّ وَالْمُهَاجِرِينَ وَالْأَنصَارِ الَّذِينَ اتَّبَعُوهُ فِي سَاعَةِ الْعُسْرَةِ مِن بَعْدِ مَا كَادَ يَزِيغُ قُلُوبُ فَرِيقٍ مِّنْهُمْ ثُمَّ تَابَ عَلَيْهِمْ ۚ إِنَّهُ بِهِمْ رَءُوفٌ رَّحِيمٌ (117)
الصفحة Page 205
(112) Mãsu tũba, mãsu bautãwa, mãsu gõdẽwa, mãsu tafiya, mãsu ruku'i, mãsu sujada mãsu umurni da alhẽri da mãsu hani daga abin da aka ƙi da mãsu tsarẽwaã ga iyãkõkin Allah. Kuma ka bãyar da bushãra ga muminai.
(113) Bã ya kasancẽwa ga Annabi da waɗanda suka yi ĩmãni, su yi istigifãri ga mushirikai, kuma kõ dã sun kasance ma'abũta zumunta ne daga bãyan sun bayyana a gare su, cẽwa lalle ne, sũ, 'yan Jahĩm ne.
(114) Kuma istigifãrin Ibrãhĩm ga ubansa bai kasance ba fãce sabõda wani wa'adi ne da ya ƙulla alƙawarinsa da shi, sa'an nan a lõkacin da ya bayyana a gare shi (Ibrãhĩm) cẽwa lalle ne shĩ (ubansa) maƙiyi ne ga Allah, sai ya barranta daga gare shi. Lalle ne Ibrahim, haƙĩƙa, mai yawan addu'a ne, mai haƙuri.
(115) Kuma Allah bai kasance mai ɓatar da mutãne a bãyan Yã shiryar da su ba, sai Ya bayyanã musu abin da zã su yi taƙawa da shi. Lalle ne Alllh, ga kõme, Masani ne.
(116) Lalle ne Allah Yanã da mulkin sammai da ƙasa, Yanã rãyarwa kuma Yanã matarwa. Kuma bã ku da wani masõyi, kuma bã ku da mataimaki, baicin Allah.
(117) Lalle ne, haƙĩƙa, Allah Ya karɓi tũbar Anbabi da Muhãjirĩna da Ansãr waɗanda suka bĩ shi, a cikin sã'ar tsanani, daga bãya zukãtan wani ɓangare daga gare su sun yi kusa su karkata, sa'an nan (Allah) Ya karɓi tũbarsu. Lalle, Shĩ ne Mai tausayi, Mai jin ƙai gare su.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022