التوبة   سورة  : At-Tawba


سورة Sura   التوبة   At-Tawba
فَلَا تُعْجِبْكَ أَمْوَالُهُمْ وَلَا أَوْلَادُهُمْ ۚ إِنَّمَا يُرِيدُ اللَّهُ لِيُعَذِّبَهُم بِهَا فِي الْحَيَاةِ الدُّنْيَا وَتَزْهَقَ أَنفُسُهُمْ وَهُمْ كَافِرُونَ (55) وَيَحْلِفُونَ بِاللَّهِ إِنَّهُمْ لَمِنكُمْ وَمَا هُم مِّنكُمْ وَلَٰكِنَّهُمْ قَوْمٌ يَفْرَقُونَ (56) لَوْ يَجِدُونَ مَلْجَأً أَوْ مَغَارَاتٍ أَوْ مُدَّخَلًا لَّوَلَّوْا إِلَيْهِ وَهُمْ يَجْمَحُونَ (57) وَمِنْهُم مَّن يَلْمِزُكَ فِي الصَّدَقَاتِ فَإِنْ أُعْطُوا مِنْهَا رَضُوا وَإِن لَّمْ يُعْطَوْا مِنْهَا إِذَا هُمْ يَسْخَطُونَ (58) وَلَوْ أَنَّهُمْ رَضُوا مَا آتَاهُمُ اللَّهُ وَرَسُولُهُ وَقَالُوا حَسْبُنَا اللَّهُ سَيُؤْتِينَا اللَّهُ مِن فَضْلِهِ وَرَسُولُهُ إِنَّا إِلَى اللَّهِ رَاغِبُونَ (59) ۞ إِنَّمَا الصَّدَقَاتُ لِلْفُقَرَاءِ وَالْمَسَاكِينِ وَالْعَامِلِينَ عَلَيْهَا وَالْمُؤَلَّفَةِ قُلُوبُهُمْ وَفِي الرِّقَابِ وَالْغَارِمِينَ وَفِي سَبِيلِ اللَّهِ وَابْنِ السَّبِيلِ ۖ فَرِيضَةً مِّنَ اللَّهِ ۗ وَاللَّهُ عَلِيمٌ حَكِيمٌ (60) وَمِنْهُمُ الَّذِينَ يُؤْذُونَ النَّبِيَّ وَيَقُولُونَ هُوَ أُذُنٌ ۚ قُلْ أُذُنُ خَيْرٍ لَّكُمْ يُؤْمِنُ بِاللَّهِ وَيُؤْمِنُ لِلْمُؤْمِنِينَ وَرَحْمَةٌ لِّلَّذِينَ آمَنُوا مِنكُمْ ۚ وَالَّذِينَ يُؤْذُونَ رَسُولَ اللَّهِ لَهُمْ عَذَابٌ أَلِيمٌ (61)
الصفحة Page 196
(55) Sabõda haka, kada dũkiyõyinsu su bã ka sha'awa, kuma haka 'ya'yansu. Abin sani kawai, Allah Yanã nufin Ya yi musu azãba, da su a cikin rãyuwar dũniya, kuma rãyukansu su fita alhãli kuwa sunã kãfirai.
(56) Kuma sunã rantsuwa da Allah cẽwa, lalle ne sũ, haƙĩƙa, daga gare ku suke, alhãli kuwa ba su zamo daga gare ku ba. Kuma amma sũ mutãne ne mãsu tsõro.
(57) Dã sunã sãmun mafaka kõ kuwa waɗansu ɓulõli, kõ kuwa wani mashigi, da sun, jũya zuwa gare shi, kuma suna gaggawar shiga.
(58) Kuma daga cikinsu akwai wanda yake zunɗen ka a kan sha'anin dũkiyõyin sadaka, sai idan an bã su daga cikinta, su yarda, kuma idan ba a bã su ba daga cikinta sai su zamo sunã mãsu fushi.
(59) Kuma dã dai su lalle sun yarda da abin da Allah Ya bã su, da ManzonSa kuma suka ce: "Ma'ishinmu Allah ne, zai kãwo mana daga falalarSa kuma ManzõnSa (zai bã mu). Lalle ne mũ, zuwa ga Allah mãsu kwaɗayi ne."
(60) Abin sani kawai, dũkiyõyin sadaka na faƙĩrai ne da miskinai da mãsu aiki a kansu, da waɗanda ake lallãshin zukãtansu, kuma a cikin fansar wuyõyi, da mabarta, da a cikin hanyar Allah da ɗan hanya (matafiyi). Farilla daga Allah. Kuma Allah ne Masani, Mai hikima.
(61) Kuma daga cikinsu akwai waɗanda suke cũtar Annabi, kuma sunã cẽwa "Shi kunne ne." Ka ce: "Kunnen alhẽri gare ku, Yanã ĩmãni da Allah, kuma Yanã yarda da mũminai, kuma rahama ne ga waɗanda suka yi ĩmãni daga gare ku."Kuma waɗanda suke cũtar Manzon Allah sunã da azãba mai raɗaɗi.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022