التوبة   سورة  : At-Tawba


سورة Sura   التوبة   At-Tawba
كَيْفَ يَكُونُ لِلْمُشْرِكِينَ عَهْدٌ عِندَ اللَّهِ وَعِندَ رَسُولِهِ إِلَّا الَّذِينَ عَاهَدتُّمْ عِندَ الْمَسْجِدِ الْحَرَامِ ۖ فَمَا اسْتَقَامُوا لَكُمْ فَاسْتَقِيمُوا لَهُمْ ۚ إِنَّ اللَّهَ يُحِبُّ الْمُتَّقِينَ (7) كَيْفَ وَإِن يَظْهَرُوا عَلَيْكُمْ لَا يَرْقُبُوا فِيكُمْ إِلًّا وَلَا ذِمَّةً ۚ يُرْضُونَكُم بِأَفْوَاهِهِمْ وَتَأْبَىٰ قُلُوبُهُمْ وَأَكْثَرُهُمْ فَاسِقُونَ (8) اشْتَرَوْا بِآيَاتِ اللَّهِ ثَمَنًا قَلِيلًا فَصَدُّوا عَن سَبِيلِهِ ۚ إِنَّهُمْ سَاءَ مَا كَانُوا يَعْمَلُونَ (9) لَا يَرْقُبُونَ فِي مُؤْمِنٍ إِلًّا وَلَا ذِمَّةً ۚ وَأُولَٰئِكَ هُمُ الْمُعْتَدُونَ (10) فَإِن تَابُوا وَأَقَامُوا الصَّلَاةَ وَآتَوُا الزَّكَاةَ فَإِخْوَانُكُمْ فِي الدِّينِ ۗ وَنُفَصِّلُ الْآيَاتِ لِقَوْمٍ يَعْلَمُونَ (11) وَإِن نَّكَثُوا أَيْمَانَهُم مِّن بَعْدِ عَهْدِهِمْ وَطَعَنُوا فِي دِينِكُمْ فَقَاتِلُوا أَئِمَّةَ الْكُفْرِ ۙ إِنَّهُمْ لَا أَيْمَانَ لَهُمْ لَعَلَّهُمْ يَنتَهُونَ (12) أَلَا تُقَاتِلُونَ قَوْمًا نَّكَثُوا أَيْمَانَهُمْ وَهَمُّوا بِإِخْرَاجِ الرَّسُولِ وَهُم بَدَءُوكُمْ أَوَّلَ مَرَّةٍ ۚ أَتَخْشَوْنَهُمْ ۚ فَاللَّهُ أَحَقُّ أَن تَخْشَوْهُ إِن كُنتُم مُّؤْمِنِينَ (13)
الصفحة Page 188
(7) Yãya wani alkawari a wurin Allah a wurin ManzonSa yake kasancẽwa ga mushirikai, fãce ga waɗanda kuka yi wa alkawari wurin Masallaci Mai alfarma? To matuƙar sun tsaya sõsai gare ku, sai ku tsayu sõsai gare su. Lalle ne Allah Yanã son mãsu taƙawa.
(8) Yãya, alhãli idan sun ci nasara a kanku, bã zã su tsare wata zumun ta ba a cikinku, kuma haka wata amãna, sunã yardar da ku da bãkunansu kuma zukãtansu sunã ƙi? Kuma mafi yawansu fãsiƙai ne.
(9) Sun saya da ãyõyin Allah, 'yan kuɗi kaɗan, sa'an nan suka kange daga hanyar Allah. Lalle ne sũ, abin da suka kasance sunã aikatãwa yã mũnana.
(10) Bã su tsaron wata zumunta a cikin mũminai, kuma haka bãsu tsaron wata amãna. Kuma waɗannan ne mãsu ta'adi.
(11) Sa'an nan idan sun tũba kuma suka tsayar da salla, kuma suka bãyar da zakka, to, 'yan'uwanku ne a cikin addini, kuma Munã rarrabe ãyõyi daki-daki, ga mutãne waɗanda suke sani.
(12) Kuma idan suka warware rantsuwõyin amãna daga bãyan alkawarinsu, kuma suka yi sũka a cikin addininku, to, ku yaki shũgabannin kãfirci. Lalle ne sũ, bãbu rantsuwõyin amãna a gare su. Tsammãninsu sunã hanuwa.
(13) Shin, bã ku yaƙin mutãne, waɗanda suka warware rantsuwõyinsu, kuma suka yi niyya ga fitar da Manzo, kuma sũ ne suka fãra muku, tun a farkon lõkaci? Shin kunã tsõron su ne? To, Allah ne marfi cancantar ku ji tsõronSa, idan kun kasance mũminai!
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022