الصافات   سورة  : As-Saaffaat


سورة Sura   الصافات   As-Saaffaat
مَا لَكُمْ كَيْفَ تَحْكُمُونَ (154) أَفَلَا تَذَكَّرُونَ (155) أَمْ لَكُمْ سُلْطَانٌ مُّبِينٌ (156) فَأْتُوا بِكِتَابِكُمْ إِن كُنتُمْ صَادِقِينَ (157) وَجَعَلُوا بَيْنَهُ وَبَيْنَ الْجِنَّةِ نَسَبًا ۚ وَلَقَدْ عَلِمَتِ الْجِنَّةُ إِنَّهُمْ لَمُحْضَرُونَ (158) سُبْحَانَ اللَّهِ عَمَّا يَصِفُونَ (159) إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ (160) فَإِنَّكُمْ وَمَا تَعْبُدُونَ (161) مَا أَنتُمْ عَلَيْهِ بِفَاتِنِينَ (162) إِلَّا مَنْ هُوَ صَالِ الْجَحِيمِ (163) وَمَا مِنَّا إِلَّا لَهُ مَقَامٌ مَّعْلُومٌ (164) وَإِنَّا لَنَحْنُ الصَّافُّونَ (165) وَإِنَّا لَنَحْنُ الْمُسَبِّحُونَ (166) وَإِن كَانُوا لَيَقُولُونَ (167) لَوْ أَنَّ عِندَنَا ذِكْرًا مِّنَ الْأَوَّلِينَ (168) لَكُنَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ (169) فَكَفَرُوا بِهِ ۖ فَسَوْفَ يَعْلَمُونَ (170) وَلَقَدْ سَبَقَتْ كَلِمَتُنَا لِعِبَادِنَا الْمُرْسَلِينَ (171) إِنَّهُمْ لَهُمُ الْمَنصُورُونَ (172) وَإِنَّ جُندَنَا لَهُمُ الْغَالِبُونَ (173) فَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ (174) وَأَبْصِرْهُمْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ (175) أَفَبِعَذَابِنَا يَسْتَعْجِلُونَ (176) فَإِذَا نَزَلَ بِسَاحَتِهِمْ فَسَاءَ صَبَاحُ الْمُنذَرِينَ (177) وَتَوَلَّ عَنْهُمْ حَتَّىٰ حِينٍ (178) وَأَبْصِرْ فَسَوْفَ يُبْصِرُونَ (179) سُبْحَانَ رَبِّكَ رَبِّ الْعِزَّةِ عَمَّا يَصِفُونَ (180) وَسَلَامٌ عَلَى الْمُرْسَلِينَ (181) وَالْحَمْدُ لِلَّهِ رَبِّ الْعَالَمِينَ (182)
الصفحة Page 452
(154) Mẽ ya same ku? Yãya kuke hukuntãwa (wannanhukunci)?
(155) Shin, bã ku tunãni?
(156) Ko kuma kunã da wani dalĩli bayyananne ne?
(157) To, ku zo da littãfinku idan kun kasance mãsu gaskiya.
(158) Kuma suka sanya nasaba a tsakãninSa da tsakãnin aljannu. Alhãli kuwa Lalle aljannu sun sani, "Lalle sũ, haƙĩƙa waɗanda ake halartarwa ne (a cikin wutã.)"
(159) Tsarki ya tabbata ga Allah daga abin da suke siffantãwa.
(160) Sai bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
(161) To, lalle, ku da abin da kuke bautãwa,
(162) Ba ku zama mãsu buwãya ba a gare Shi.
(163) Sai wanda yake mai shiga babbar wutã Jahĩm.
(164) "Kuma bãbu kõwa daga cikinmu, fãce yanã da matsayi sananne."
(165) "Kuma lalle mu, haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin sahu-sahu (dõmin ibãda)."
(166) "Kuma lalle mũ haƙĩƙa, mũ ne mãsu yin tasbĩhi."
(167) Kuma lalle sũ, sun kasance sunã cẽwa,
(168) "Dã lalle munã da wani littãfi irin na mutãnen farko."
(169) "Lalle dã mun kasance bãyin Allah waɗanda aka tsarkake."
(170) Sai suka kãfirta da shi. Sabõda haka zã su sani.
(171) Kuma lalle, haƙĩƙa kalmarMu ta gabãta ga bãyinMu, Manzanni.
(172) Lalle sũ, haƙĩƙa, sũ ne waɗanda ake taimako.
(173) Kuma lalle rundunarMu, haƙĩƙa, sũ ne marinjaya.
(174) Sabõda haka juya daga barinsu, har a wani lõkaci.
(175) Ka nũna musu (gaskiya), da haka zã su dinga gani.
(176) Shin fa, da azabarMu suke nẽman gaggãwa?
(177) To, idan ta sauka ga farfãjiyarsu, to, sãfiyar wadanda ake yi wa gargaɗi ta mũnana.
(178) Kuma ka jũya daga barinsu har a wani lõkaci.
(179) Ka nũna (musu gaskiya), da haka zã su dinga nũnãwa.
(180) Tsarki ya tabbata ga Ubangijinka, Ubangijin rinjãye, daga barin abin da suke siffantãwa.
(181) Kuma aminci ya tabbata ga Manzanni.
(182) Kuma gõdiya ta tabbata ga Allah Ubangijin halittu.
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022