الصافات   سورة  : As-Saaffaat


سورة Sura   الصافات   As-Saaffaat
مَا لَكُمْ لَا تَنَاصَرُونَ (25) بَلْ هُمُ الْيَوْمَ مُسْتَسْلِمُونَ (26) وَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ (27) قَالُوا إِنَّكُمْ كُنتُمْ تَأْتُونَنَا عَنِ الْيَمِينِ (28) قَالُوا بَل لَّمْ تَكُونُوا مُؤْمِنِينَ (29) وَمَا كَانَ لَنَا عَلَيْكُم مِّن سُلْطَانٍ ۖ بَلْ كُنتُمْ قَوْمًا طَاغِينَ (30) فَحَقَّ عَلَيْنَا قَوْلُ رَبِّنَا ۖ إِنَّا لَذَائِقُونَ (31) فَأَغْوَيْنَاكُمْ إِنَّا كُنَّا غَاوِينَ (32) فَإِنَّهُمْ يَوْمَئِذٍ فِي الْعَذَابِ مُشْتَرِكُونَ (33) إِنَّا كَذَٰلِكَ نَفْعَلُ بِالْمُجْرِمِينَ (34) إِنَّهُمْ كَانُوا إِذَا قِيلَ لَهُمْ لَا إِلَٰهَ إِلَّا اللَّهُ يَسْتَكْبِرُونَ (35) وَيَقُولُونَ أَئِنَّا لَتَارِكُو آلِهَتِنَا لِشَاعِرٍ مَّجْنُونٍ (36) بَلْ جَاءَ بِالْحَقِّ وَصَدَّقَ الْمُرْسَلِينَ (37) إِنَّكُمْ لَذَائِقُو الْعَذَابِ الْأَلِيمِ (38) وَمَا تُجْزَوْنَ إِلَّا مَا كُنتُمْ تَعْمَلُونَ (39) إِلَّا عِبَادَ اللَّهِ الْمُخْلَصِينَ (40) أُولَٰئِكَ لَهُمْ رِزْقٌ مَّعْلُومٌ (41) فَوَاكِهُ ۖ وَهُم مُّكْرَمُونَ (42) فِي جَنَّاتِ النَّعِيمِ (43) عَلَىٰ سُرُرٍ مُّتَقَابِلِينَ (44) يُطَافُ عَلَيْهِم بِكَأْسٍ مِّن مَّعِينٍ (45) بَيْضَاءَ لَذَّةٍ لِّلشَّارِبِينَ (46) لَا فِيهَا غَوْلٌ وَلَا هُمْ عَنْهَا يُنزَفُونَ (47) وَعِندَهُمْ قَاصِرَاتُ الطَّرْفِ عِينٌ (48) كَأَنَّهُنَّ بَيْضٌ مَّكْنُونٌ (49) فَأَقْبَلَ بَعْضُهُمْ عَلَىٰ بَعْضٍ يَتَسَاءَلُونَ (50) قَالَ قَائِلٌ مِّنْهُمْ إِنِّي كَانَ لِي قَرِينٌ (51)
الصفحة Page 447
(25) Me ya sãme ku, bã ku taimakon jũna?
(26) Ã'a, sũ a yau, mãsu sallamãwa ne.
(27) Kuma sãshensu ya fuskanta ga sãshe, sunã tambayar jũna.
(28) Suka ce: "Lalle kũ, kun kasance kunã jẽ mana daga wajen dãma (inda muka amince)."
(29) Suka ce: "Ã'a, ba ku kasance mũminai ba.
(30) "Kuma wani dalĩli bai kasance ba gare mu a kanku. Ã'a, kun kasance mutãne ne mãsu kẽtare iyãka."
(31) "Sabõda haka maganar Ubangijinmu ta wajaba a kanmu. Lalle mũ, mãsu ɗanɗanãwa ne."
(32) "Sabõda haka muka ɓatar da ku. Lalle mũ, mun kasance ɓatattu."
(33) To lalle sũ a rãnar nan, mãsu tãrayya ne a cikin azãbar.
(34) Lalle Mũ, kamar haka Muke aikatãwa game, da mãsu laifi.
(35) Lalle sũ, sun kasance idan an ce musu: "Bãbu abin bautãwa, fãce Allah," sai su dõra girman kai.
(36) Kuma sunã cẽwa, "Shin, mũ lalle mãsu barin gumãkanmu ne, sabõda maganar wani mawãƙi mahaukaci?
(37) Ã'a, yã zo da gaskiya kuma ya gaskata Manzanni.
(38) Lalle kũ, haƙĩƙa mãsu ɗanɗana azãba mai raɗaɗi ne.
(39) Kuma bã zã a sãka muku ba fãce da abin da kuka kasance kunã aikatãwa.
(40) Fãce bãyin Allah waɗanda aka tsarkake.
(41) Waɗannan sunã da abinci sananne.
(42) 'Ya'yan itãcen marmari, kuma sunã waɗanda ake girmamãwa.
(43) A cikin gidãjen Aljannar ni'ima.
(44) A kan karagu, sunã mãsu fuskantar jũna.
(45) Anã kẽwayãwa a kansu da hinjãlan giya, ta daga waɗansu marẽmari.
(46) Farã mai dãɗi ga mashãyan.
(47) A cikinta bãbu jirĩ kuma ba su zama mãsu mãye daga gare ta ba,
(48) Kuma a wurinsu, akwai mãtan aure mãsu taƙaita kallonsu, mãsu manyan idãnu.
(49) Kamar dai su ƙwai ne ɓõyayye.
(50) Sai sãshensu ya fuskanta a kan sãshe, sunã tambayar jũna.
(51) Wani mai magana daga cikinsu ya ce: "Lalle ni wani abõki ya kasance a gare ni (a dũniya)."
 


اتصل بنا | الملكية الفكرية DCMA | سياسة الخصوصية | Privacy Policy | قيوم المستخدم

آيــــات - القرآن الكريم


© 2022